Kano: An yi taron inganta sana’o’in gargajiya a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

Himma da hoɓɓasa ta Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na cigaba da gudana a kowane fanni na bunkasa cigaban al’umma.

Akan haka ne Karamar Hukumar Bichi ta yi gangamin taron zaburar da ma’abota sana’o’In gargajiya na ɗaukacin karamar hukumar.

A wata sanarwa da Jami’ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi R/Lemo ta fitar, ta ce taron ya ƙunshi masu sana’o’i daban-daban da suka haɗa da; abinci, saka, rini, ƙira da kaɗe-kaɗen gargajiya da ake kira da Kalankuwa.

Bisa wannan gagarumin biki na farfado da al’adu da sana’o’in gargajiya na faɗin jihar da gwamati ke ƙoƙarin yi, karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, a ranar 25 zuwa 27 ga watan Oktoba na shekara ta 2025, Karamar Hukumar Bichi ta ɗaura ɗamarar taryar wannan babban taro mai zuwa.

Don haka ne ta gayyaci dukkan masana’antan da suka shafi wannan bigire.

Malam Muntari Yahaya Saye, ƙwararre a fannin saka, musamman kayan masarautu da kuma fitacce daga Makerar Farfaru bangaren makamai na gargajiya, wato Malam Bala Yusuf Kargon Bichi a Mazabar Muntsira, tare da makeri Malam Sulaiman Abdu Waire da ya shahara a fannin kera garmar shanu, fatanya, magirbi da sauransu. Dukkansu sun yi karin haske a yayin nuna fasaharsu ta irin wadannan hajojin nasu.

“Wannan kuma shi ne mudukare ake masa kirari zanin Fulani” Malam Muntati Yahaya Saye.
“Wannan muna kiranta kankama ta yankan shanu.” Malam Bala Ysuf.
“Ni kadai haka idan na zauna a makera zan kera ma wukake sha biyar (15).” Malam Sulaiman Abdu

Ɓangaren kade-kade na waƙoƙin gargajiya ma sun nuna irin salon tasu basirar a yayin kwarya-kwaryar wannan taro na share fage, inda muka ji daga mawakin kada Duman-Girke, Ibrahim Damargu.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Abubakar Sulaiman Babangida Danzabuwa, da ya wakilci shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata da kuma Sakataren Mulki, Hon Anas Muhammad Abdullahi, tare da Daraktan Mulki, Alhaji Abba Muhammad Diso, sun ce Karamar Hukumar Bichi a shirye take ta bai wa masu sana’ar gargajiyar gudunmawa dari bisa dari, sun kuma ba su shawarar zuwa a kungiyance, ga Hukumar Kasuwar Zamani ta Bichi domin neman tallafin shagunan da za su ci gaba da gudanar da sana’o’insu.

Haka ma Shugaban Sashen Jin Dadi da Walwalar Jama’ar Bichi, Malam Ibrahim Isyaku Shanono, ya tabbatar da kudurin gwamnati ga wannan taro.

“Kowace karamar hukuma an ce ta gabatar da rahasal na abubuwan da ta tura, wanda take gudanarwa na gargajiya walau; sana’o’i ko abinci na gargajiya da makadan gargajiya.” Malam Ibrahim Isyaku Shanono.

By Babaji