Shugaban ACF ya caccaki masu yi wa Matatar Dangote zagon ƙasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), Alhaji Bashir Dalhatu, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira da zagon ƙasa da gangan da ake yi wa Matatar Mai ta Dangote.

Yayin taron Kwamitin Amintattu da aka gudanar a Kaduna ranar Talata, Dalhatu ya ce matsalolin da ake fuskanta a wannan babbar ma’aikata da aka kammala kwanan nan “abin mamaki ne kuma abin takaici ƙwarai.”

Ya zargi “ƙungiyoyin ma’aikata marasa kishin ƙasa, tare da wasu masu hannu a ɓoye,” da ƙoƙarin lalata wannan muhimmin ginshiƙin tattalin arzikin ƙasa.

A cewarsa, “Dole a faɗa wa waɗannan mutane a fili cewa suna aiki ne don maƙiyan Nijeriya da ‘yan ƙasa gaba ɗaya — na yanzu da waɗanda ba a haifa ba.”

Dalhatu ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki gaggawar mataki don kare Matatar Dangote, wadda ya bayyana a matsayin alamar fata ta farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa.

Haka kuma, ya yaba wa dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewarsu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Arewacin Nijeriya. Ya ce ACF tana “cike da godiya ga maza da mata masu sanye da kaki da ke sadaukar da rayukansu domin kare yankin da ƙasar baki ɗaya.”

Sai dai ya buƙaci shugabannin soji da su ci gaba da duba dabarunsu, domin rage asarar rayuka da kuma tabbatar da cewa suna gaba da duk wata barazana da ka iya tasowa.

Dalhatu ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu manyan jami’an ACF a matakan ƙasa da jihohi ke fitar da bayanai masu karo da juna ga kafafen watsa labarai.

Ya ce, “Yanzu ACF na matuƙar buƙatar tsarin da zai tsara yadda jami’anta ke magana da manema labarai game da harkokin ƙungiya.”

A taron an kuma tattauna shirye-shiryen bikin cika shekara 25 da kafuwar ACF, wanda za a gudanar da shi a Kaduna daga 20 zuwa 22 ga watan Nuwamba, 2025.

Dalhatu ya ce, wannan biki zai zama babbar dama ta “sake daidaita ƙungiyar domin ta fi tasiri a gaba.”

Haka kuma, Majalisar ta nuna damuwa kan yawaitar ƙungiyoyin da ke tasowa a Arewacin ƙasar da ke da manufofi makamancin na ACF, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya raba kai da raunana murya ɗaya ta yankin.

“ƙarfina yana cikin haɗin kai, cikin tara albarkatu tare da yin magana da murya guda kan duk wani lamari da ya shafi mutanenmu,” inji Dalhatu.

A yayin da ake gab da zaɓen 2027, shugaban ACF ya sake jaddada matsayin ƙungiyar na rashin shiga jam’iyyun siyasa kai tsaye, ko da yake ya bayyana cewa kowane memba na da ‘yancin zama cikin jam’iyyar da yake so.

Ya ce,“Kodayake wasu ‘yan ACF na iya kasancewa cikin jam’iyyun siyasa daban-daban, ƙungiyar kanta ba za ta nuna son kai ga wata jam’iyya ba.”

A ƙarshe, Dalhatu ya tabbatar da cewa ACF za ta cigaba da goyon bayan dimokuraɗiyya mai inganci, kyakkyawan shugabanci da kuma haɗin kan Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi