Mawaƙi Ghali El-Abdallah DZ ya zama shugaban gidan talabijin na Hijrah

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

Hukumar gudanarwa ta tashar gidan talabijin ta Hijrah Tv ta tabbatar da nadin Ghali El-Abdallah DZ a matsayin sabon Manajan Darakta na tashar wato (MD)

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da hukumar gidan Talbijin ɗin suka rabawa manema labarai, Shugaban gidan talbijin na Hijrah a cikin sanarwar ya ce sun yi wannan nadin duba da irin gwagwarmayar da Ghali El-Abdallah DZ ya yi a gidajen rediyo da dama da kuma gwagwarmayar da ya yi a masana’antar Kannywood.

Wannan dalilai ya sa suka tabbatar da yana da muhimmiyar gudunmawar da zai bai wa tashar Hijrah TV a irin wannan lokaci.

Ghali El-Abdallah dai fitaccen mawaƙi ne furodusa kuma jarumi a Kannywood, wanda aka haifa a Unguwar Durumin Zungura dake cikin birnin Kano, a shekarar 1978 inda ya yi makarantar firamare ɗin sa a Kwalli kuma ya yi ƙaramar sakandare a Sabuwar Kofa sai babbar sakandare a Kwalejin Rumfa duk a cikin birnin Kano. 

Ya ci gaba a Kwalejin Sa’adatu Rimi inda ya yi NCE. Sai kuma ya tafi Jami’ar Bayero inda ya yi babbar difloma a fannin aikin jarida.

A ɓangaren aiki kuwa ya yi aiki a gidan rediyon Freedom FM da gidan rediyon Rahama FM da gidan rediyon Arewa, sai Kannywood Series T V , da kuma Hijira TV Wanda a yanzu yake a matsayin Manajan Darakta.

A Masana’antar Kannywood kuma Ghali El-Abdallah D Z ya kasance komai da ruwan ka. Inda ya fara da waƙoƙin tallace-tallace, da na wayar da kai. Sai kuma shirin sa mai farin jini na ‘Dandalin Fasaha’ wanda yake hira da wawaƙa da ‘yan fim. 

Sannan shi ne marubuci kuma jagoran shirya wasan kwaikwayo na Birnin Dala a Dala FM, sai kuma wasan kwaikwayo na ‘ƙasar Jallaba’ a tashar Arewa FM wadda daga baya aka yi fim ɗin wasan kwaikwayon da sunan ‘Mai martaba’ , fim ɗin da ya shiga jerin finafinan da suka wakilci Nijeriya a gasar Oscar a ƙasar Amerika.

By ukarofi