Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da tattaunawa da kamfanin ƙasar Chana don yaƙar Lakurawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kebbi ta jaddada aniyarta ta cigaba da aiki tare da dakarun sojoji, ƴan sanda da wasu hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ga al’umma a sassan jihar.

A baya ne Gwamna Dakta Nasir Idris na jihar ya karɓi baƙoncin tawagar tsaro ta G-Safety domin haɗa hannu da ita wajen ganin ta faɗaɗa ayyukanta na daƙile matsalolin ta’addanci a jihar.

A ranar Laraba gwamnan ya karɓi tawagar ta ƴan Chana da nufin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi dabarun daƙile ta’addanci da ƙarfafa wa hukumomin tsaro a jihar.

Gwamnan, wanda ya karɓi tawagar a Gidan Gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, ya bayyana ziyarar a matsayin abinda ke da muhimmanci ga al’amuran tsaro musamman a fannin bayanan sirri da samar da mafita ga ayyukan ƴan ta’adda a jihar.

Haka kuma, Gwamnatin ta ce babu wata yarjejeniya ko kwangila da aka ƙulla da kowanne kamfanin tsaro na kasashen waje, kamar yadda wasu rahotanni ke nunawa.

Don haka rahoton da ke yawo akan haka ba gaskiya ba ne, abu ne da ke da nufin ɓata suna kuma jama’a su yi watsi da shi, kamar Sakataren yaɗa labaran gwamnatin ya bayyana.

By Babaji