
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaddamar da kwamitin sanya ido akan harkokin jiragen sama domin aikin Hajjin 2026.
An ƙaddamar da kwamitin ne a wani taro da aka gudanar a Hajj House da ke Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kirayi mambobin kwamitin da su yi aiki bisa gaskiya da kishin al’umma, tare da tabbatar da cewa dukkan shirye-shiryen jiragen sama na tafiya da dawowar alhazai sun kasance akan tsari da kuma aminci.
Ya bayyana cewa, gwani Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar aikin Hajji a matsayin amana ta addini saboda haka wajibi ne a tabbatar da jin-daɗin alhazai.
Da yake jawabi, Kwamishinan Ayyuka da bada Lasisi, Frins Anofi Olanrewaju Elegushi, ya ce kwamitin zai yi aiki don ganin cewa dukkan alhazai sun tashi cikin tsaro, mutunci da kima, ba tare da wata barazana ba.
Kwamitin zai kuma duba shirye-shiryen filayen jirage, tantance kamfanonin jiragen sama, da kuma kula da ingancin hidimar da ake bayarwa ga alhazai.
Kazalika, Shugaban na NAHCON ya ja hankalin mambobin kwamitin da cewa idon miliyoyin Musulman Nijeriya na kansu don haka su ɗauki aikin a matsayin amana akansu.
