Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban kuma wanda ya assasa kamfanin ASIA Group of Companies wato Alhaji Sani Isah Abubakar (ASIA) ya samu Digirin Girmamawa na (Doctor of Excellence – Honoris Causa) daga British American University, a matsayin yabo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasuwanci, jagoranci, da ayyukan jin ƙai.
An gabatar da wannan taron lambar yabo ne a wani biki da kamfanin ASIA Group ya shirya a garin Kano ranar Alhamis, wanda ya ja hankalin manyan baƙi, sarakunan gargajiya, shugabannin kasuwanni da fitattun mutane daga sassan ƙasar nan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Abubakar Sadiq Muhammad, mai taimaka wa shugaban wajen harkokin yaɗa labarai, ya fitar kuma ya miƙa ga jaridar Blueprint Manhaja a ranar Talata.
A cewar sanarwar, taron ya kasance na girmamawa da tunawa da manyan nasarorin da Alhaji Abubakar ya cimma, da irin tasirin da ya bayar wajen haɓaka harkokin kasuwanci da walwalar al’umma a Najeriya.
Masu halarta sun bayyana wannan biki a matsayin haɗuwar imani, ƙwazon aiki, da hangen nesa, domin girmama mutum wanda rayuwarsa ta kasance abin koyi na gaskiya, jajircewa, da kishin ƙasa.
A jawabinsa na karɓar lambar yabo, Alhaji Abubakar ya bayyana godiyarsa ga Allah maɗaukaki tare da sadaukar da wannan girmamawa ga ma’aikata, abokan hulɗa, da masu goyon bayan ASIA Group.
“Alhamdulillah, taron ya kasance cikin nasara. Wannan girmamawa ba tawa kaɗai bace; ta duk ma’aikata, abokan hulɗa, da masu goyon bayan ASIA Group ce. Tare muke gina tarihi na kasuwanci, taimako, da hidima ga ɗan Adam,” in ji shi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ASIA Group ta zama ɗaya daga cikin manyan kamfanoni masu bunƙasa da faɗaɗa ayyukansu a Najeriya, tana da jarin saka hannun jari a fannonin kasuwanci, masana’antu, makamashi mai sabuntawa, sufuri, da ci gaban al’umma.
Kazalika, kamfanin ya jaddada aniyarsa ta ƙirƙirar damar aikin yi, tallafawa matasa, da goyon bayan shirye-shiryen ci gaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
Kamfanin ya kuma miƙa godiya ga baƙi, kafafen yaɗa labarai, da jama’ar Kano bisa goyon bayan da suka bayar, yana mai cewa wannan girmamawa za ta ƙara ƙarfafa himmarsu wajen ƙirƙira da haɓaka ci gaba mai haɗa kai.
“Wannan ci gaban shi ne mataki na farko kawai,” in ji Abubakar. “ASIA Group za ta ci gaba da yin aiki da gaskiya, hangen nesa da sadaukarwa — domin ci gaban Najeriya, Afirka, da ɗan Adam baki ɗaya.”
ASIA Group of Companies dai, da ke da hedikwata a Kano, na daga cikin manyan ƙungiyoyin kasuwanci na Najeriya da ke gudanar da ayyukansu bisa tubalin gaskiya, ƙirƙira, da tasiri ga al’umma.
