Yara 274,866 suka amshi allurar rigakafi a ƙaramar hukumar Bichi

Spread the love

Jami’in gudanar da aikin rigakafi a yankin, Malam Mahmuda Garba ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da jami’ar yaɗa labarai ta karamar hukumar.

Allurar rigakafin da ta ƙunshi ta Kansar Mahaifa, Kyanda da cutar Shan Inna, da aka gudanar daga 7 ga watan Oktoba zuwa 17 ga watan, ya ce an kammala aikin cikin nasara a sassan ƙaramar hukumar.

“Mun yi aikinmu gaskiya babu wata matsala, wasu kaso 80 ne bisa ɗari wasu kuma kaso 80 da wani ne, wanda duk ya kai kaso 90 to ya yi aikinsa, kaso 94/100 muka yi a aikinmu na rigakafi.” In ji shi.

Malam Mahmuda ya ƙara da cewa kimanin yara 173,158 ne suka amfana da allurar rigakafin Kyanda, inda yara 99, 639 suka samu tagomashin allurar rigakafin cutar Shan Inna, da kuma yara mata da suka rabauta da allurar rigakafin Kansar Mahaifa 2,069 a ƙaramar hukumar ta Bichi.

Jami’in, ya ci gaba da cewa an gudanar da aikin rigakafin ya kasance a wurare da suka hadar da; gidaje, makarantu, ƙofar gidajen dagatai, masu unguwanni da masu faɗa a ji a dukkan mazaɓu 11 na garin Bichi.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata da Shugaban sashen lafiya, Malam Kabir Abubakar Gwarzo da Kansilan Lafiya, Hon. Bashir Sabi’u Magaji Saye na yankin, sun yaba tare da gode wa al’umar Bichi; jami’an gudanar da aikin da waɗanda suka amfana bisa haɗin kan da ƙaramar hukumar ta cim ma wannan gagarumar nasara.

“Mun samu wannan nasara ne saboda tallafin ma’aikatanmu da suka jajirce.” Kabir Abubakar Gwarzo

By ukarofi