Masu dillacin filaye da gidaje na gaskiya na da kyakkyawar alaƙa da masarautu – Shatiman ƙasa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa masu dillanci ƙasa amintattu na gaskiya, waɗanda ke cinikayya da filaye, gidaje, mai da sauransu, suna da kyakkyawar alaƙa da masarautu kamar sarakuna, hakimai, masu unguwanni da sauran hukumomi. Wannan ya sa Shatiman ƙasa kuma Shatiman ƙasar Hausawa ta Afirka, Alhaji Salihu Sagir Ayagi, ya kai ziyara ga Hakimin Dawakin Kudu, Alhaji Abba Yusuf, wanda kuma shi ne sakataren masarautar Kano.

Ya ce kyakkyawar alaƙarsa da Hakimin Dawakin Kudu ta samo asali ne tun shekaru 25 da suka wuce lokacin da yake harkar kasuwanci a yankin. Ya bayyana cewa suna zaune lafiya da jama’a, suna taimakawa da al’umma ta fannin lafiya, samar da lantarki, da tallafin marayu.

Shi kuwa shugaban masu sayar da gidaje da filaye a Kano ƙarƙashin KAPADA, Isah Jibrin Kaci ƙasa, ya bayyana a wani gagarumin taro cewa suna murna da haɗin kan ’yan kasuwa domin ƙarfafa su wajen yin rajistar zaɓe, saboda muhimmancinsa ga siyasar ƙasar.

By ukarofi