
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta musanta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa jami’ar tana da hannu wajen haɗa makamin nukiliya a ɓoye ga Nijeriya.
Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Ya ce bidiyon da aka ƙirƙira ta fasahar zamani wato AI, ƙarya ne da ke da nufin ruɗar da jama’a game da shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da Nijeriya ke gudanarwa.
Ya ce, bidiyon ya yi ikirarin cewa masana kimiyyar Nijeriya a shekarun 1980 sun kera sinadarin ‘uranium’ mai hatsarin gaske a Kaduna, tare da samun kayan aiki daga ƙungiyar AQ Khan ta Pakistan, lamarin da jami’ar ta bayyana a matsayin ‘batu marar tushe ko hujja’.
Daraktan ya bayyana cewa, a lokacin da ake magana, yawancin masana kimiyya na cibiyar “Energy Research and Training (CERT)” a jami’ar suna ci gaba da karatu a ƙasashen waje, don haka ba zai yiwu su shiga irin wannan aiki ba.
Ya kara da cewa ABU ba ta taba samun wani kayan aikin gina makamin nukiliya daga kowace ƙasa ba, kuma cibiyar makamashin da take da ita a wancan lokaci ita ce injin “14 MeV Neutron Generator” wanda aka kunna a 1988.
Ya kuma bayyana cewa na’urar farko ta nukiliya a Nijeriya (NIRR-1) an kafa ta ne a 1996 karkashin shirin hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), kuma aka fara amfani da ita a 2004.
Umar ya tabbatar da cewa dukkanin ayyukan nukiliyar Najeriya na zaman lafiya ne, bisa ka’idodin yarjejeniyar hana yada makaman nukiliya (NPT) da yarjejeniyar Pelindaba.
Kazalika, ya ce ABU tun kafuwarta tana aiki ne don ci-gaban kimiyya da fasaha domin amfanin ɗan-adam, ba ƙera makaman yaƙi ba har ma ace nukiliya.
