Ƙungiyar Wamban Shinkafi ta yi kira ga Tinubu ya hana Matawalle amfani da ofishinsa don siyasa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressive Congress APC, ɓangaren ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front a jihar Zamfara, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa da su hana ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle amfani da ofishin sa wajen gudanar taron siyasa.

Yushau Abdullahi Mada
Shugaban ƙungiyar Democratic Front Wamban Shinkafi ya yi wannan kira a Gusau yau ranar Asabar.

A cewarsa, kiran ya zama dole idan aka yi la’akari da cewa, ofishin Ministan ba don siyasa aka kafashi ba, sai don kare ƙasa daga dukkanin ƙalubalen rashin tsaro a faɗin Nijeriya.

Yushau ya sake jaddada cikakken goyon bayansu ga Dr sani Abdullahi Shinkafi.

Ƙungiyar ta bayyana Shinkafi a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan APC, waɗanda suka sadaukar da kansu wajen yaƙi da rashin adalci a jihar Zamfara.

Yusha’u Abdullahi Mada ya bayyana cewa Dr. Sani Abdullahi Shinkafi mutum ne jajirtacce idan aka yi la’akari da yadda yake tafiyar da salon siyasa a jihar.

Magoya bayan Shinkafin hakazalika sun sake jaddada ƙudirin su na tabbatar da adalci a jam’iyyar All Progressive Congress APC reshen jihar Zamfara.

A cewarsa, ƙungiyar za ta goyi bayan duk wani ɗan takarar gwamna da zai fito daga Zamfara ta yamma a shekarar 2027 ba.

“Zamu goyi bayan sauyin mulki ne kawai don samar da ɗan takarar gwamna daga Zamfara ta yamma a shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, don tabbatar da adalci ga kowane yanki.” Ya jaddada.

By ukarofi