Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Tsohon Shugaban ƙungiyar Matasa ta ƙasa reshen jihar Gombe kuma tsohon shugaban ƙungiyar Zabi Sonka da taimakon juna a jihar Gombe, Kwamared Garba Ubale, ya sha alwashin haɗe kan ‘ya’yan ƙungiyar idan aka zaɓe shi.
‘Ya’yan ƙungiyar daga yankin Arewa maso Gabas ne suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da wakilinmu a shirye-shiryen ƙungiyar na zaɓenta na ƙasa.
Mambobinta ƙungiyar daga sassa daban-daban na ƙasar suka nuna cikakken goyon baya ga Kwamared Garba Muhammad Ubale domin ya jagoranci ƙungiyar a matakin ƙasa.
Kwamared Garba, wanda ya shahara wajen shiryar da matasa da gina hacin kai a tsakanin al’umma, ya taɓa zama Shugaban Majalisar Matasa ta ƙasa (NYCN) reshen Jihar Gombe da kuma Shugaban Zaɓi Sonka a jihar. A cewar mambobi, shugabancinsa ya kasance abin misali na gaskiya, himma da sadaukarwa.
Suka ce a ƙarƙashin jagorancinsa a Gombe, an gudanar da taron ƙasa na farko na ƙungiyar a shekarar 2009, wanda ya haɗa mambobi sama da 2,000 daga faɗin ƙasar. Fiye da rabinsu ya sauke su da kuɗinsa na kansa, abin da ya tabbatar da kishinsa da jajircewarsa ga ci gaban ƙungiyar.
Da yake tsokaci kan manufofinsa, Kwamared Garba ya bayyana cewa idan ya samu damar jagoranci, zai mayar da hankali wajen sabunta tsarin ƙungiyar domin ta zama mai tasiri a fannonin aikin sa kai, tarbiyya da haɓaka kishin ƙasa tsakanin matasa.
Ya ce ƙungiyar za ta sake fitowa fili a matsayin abin koyi ga sauran ƙungiyoyin matasa a Nijeriya.
Ya kuma yi alƙawarin haɗa kai da hukumomin gwamnati kamar Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA), Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Cigaban Matasa don ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da shimfiɗa ta zuwa dukkan jihohi.
Ya ƙara da cewa, zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kafafen yaɗa labarai, musamman Radio Nigeria Kaduna da sauran gidajen rediyo a faɗin ƙasar, domin tallata shirye-shiryen ƙungiyar kamar aikin gayya da wayar da kan jama’a, tare da sabunta martabar ƙungiyar a matsayin ginshiƙin kishin ƙasa da hidimar al’umma.
