
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, ta karɓi baƙoncin shugaban ƴan Sandan ƙaramar hukumar, wato CSP Murtala Muhammad Fagan tare da muƙarrabansa.
A wata sanarwa da jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar wa manema labarai, DPOn, wato CSP Murtala Muhammad, da yake jawabin a ofishin Ciyaman ɗin Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya bayyana maƙasudin ziyarar, wanda shine gabatar da sababbin ma’aikata na jami’an tsaro na ƴan asalin ƙaramar hukumar da suka rabauta da tura su ainahin ƙaramar hukumarsu aiki su 14 domin sanin makamar aiki.
Shi ma a nasa jawabin shugaban ƙaramar hukumar, ya ja hankalin sababbin ƴan sandan da su zama masu kyawawan dabi’u a dukkan harkokin ayyukansu.
Sannan su tabbata da tsare gaskiya da adalci gami da riƙon amana bakin bakin ayyukansu.
Ya kuma yi musu nasiha da kada su yi amfani da aikinsu wajen cin zarafi ko musguna wa jama’a ko da kuwa ɓangaren wadanda suka taba samun wata matsala ko saɓani da su a tsakaninsu ta fuskar mu’amalar rayuwa ta yau da kullum duba da dukkan ɗan-adam ajizi ne.
A ƙarshe, ya yi musu fatan alheri da gama aiki lafiya a cikin nasara da fatan cigaba da kasancewa cikin aminci.


