Wata mata ta kai zafin rana ƙara ofishin ’yan sanda a Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta haifar da abin mamaki a jihar Legas, bayan ta shiga ofishin ‘yan sanda na Panti domin kai ƙara kan zafin rana da ta ce ya yi tsanani sosai.

Rahotanni daga wani mai amfani da shafin ɗ (tsohon Twitter) mai suna Olamide (@Olamide0fficial) sun bayyana cewa matar ta ɗauki motar haya ta Uber daga Lekki zuwa Panti, inda ta ce za ta kai ƙara saboda yanayin zafi ya yi “tsauri fiye da kima.”

Sai dai bayan isarta ofishin ‘yan sandan, matar ta ƙi biyan kuɗin shatar motar na N15,000 da direban Uber ya nema. Lamarin ya sa wani ɗan sanda ya biya kuɗin motar don kada a sami rikici.

Bayan an biya kuɗin, matar ta ƙi barin ofishin, inda ta ce tana son “hayar ɗaki” a cikin ofishin ‘yan sandan.

A cewar Olamide a shafinsa na ɗ, “Wata mata ta ɗauki Uber daga Lekki zuwa Panti don kai ƙara kan zafin rana, ta ƙi biyan direban Uber N15,000. Wani ɗan sanda ya biya mata kuɗin, amma daga baya ta dawo ta ce tana so ta kama gida a cikin ofishin ‘yan sandan.”

‘Yan sandan da ke bakin aiki sun ruɗe, suna mamakin yadda za su karɓi ƙara daga mutum kan rana — wato wani abin halitta da ba shi da adireshi.

Daga bisani, ofishin ya sanar da Ma’aikatar Harkokin Matasa da Ci gaban Jama’a ta Jihar Legas, wadda ta tura tawagar ceto ta Rapid Rescue Team ɗinta cikin gaggawa bayan samun bayanin ta hanyar Instagram.

Tawagar ta je cikin mintuna kaɗan, ta kwantar da matar cikin natsuwa, sannan ta kai ta cibiyar kula da masu buƙatar taimakon ƙwaƙwalwa ta jihar, inda take samun kulawar likitoci da masu ba da shawara kan lafiya ta kwakwalwa.

Wani jami’in ofishin ya ce, “Da farko matar ta yi kama da wacce ke da lafiya — tufafi masu tsada, jaka mai kyau, kwalliya cikakke. Amma daga bisani ta fara nuna rana tana cewa ‘Wannan abin sama ba zai bar ni ba!’ Mun rasa dariya za mu yi ko kuka.”

Kwamishinan Harkokin Matasa na jihar, Hon. Mobolaji Abubakre Ogunlende, ya yaba da yadda tawagar ta yi aiki cikin sauri, yana cewa, “Wannan shi ne dalilin da ya sa muke da ƙungiyar ceto a ko da yaushe. Matsalolin lafiyar kwakwalwa ba sa sanarwa kafin su faru, amma saurin rahoto daga jama’a yana iya ceton rayuka.”

Shi kuma Babban Sakatare na Ma’aikatar, Pharm. (Mrs.) Toyin Oke-Osanyintolu, ta jaddada muhimmancin shirin gwamnati na “See Something, Say Something” (Idan ka gani, ka faɗa), tana roƙon jama’a da su rika sanar da hukumomi idan sun ga wani cikin halin damuwa.

Ta ce, “Saƙon Instagram guda ɗaya ya ceci rai yau. Kada ka yi jinkiri — kira 0913 205 5075; gargaɗin ka na iya zama damar ceton rayuwar wani.”

Likitoci a cibiyar sun tabbatar cewa matar tana amsar magani yadda ya kamata, kuma danginta suna hanyarsu ta zuwa Legas don ɗaukar nauyin kula da ita.

By ukarofi