Dangote ya zama ɗan Afrika na farko da ya mallaki Dala biliyan 30

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya kafa sabon tarihi bayan ƙididdigar Bloomberg Billionaires Indeɗ ta nuna cewa dukiyarsa ta kai Dala Biliyan 30.2, wanda ya fi kowanne mutum a nahiyar Afirka.

Rahoton ya nuna cewa, Dangote ya ƙara dala biliyan 2.25 cikin shekara guda — ƙaruwa da kashi 8% – sakamakon ribar da ya samu daga harkokin siminti, man fetur, da takin zamani.

Bloomberg ta bayyana cewa dukiyarsa ta ƙaru da dala miliyan 89.2 cikin sa’o’i 24 kacal, lamarin da ya tabbatar da matsayin sa a matsayin mutum na 75 mafi arziki a duniya.

A matakin duniya, Dangote ya shiga jerin manyan attajirai irin su Gina Rinehart, Eyal Ofer, da Hasso Plattner, waɗanda dukkaninsu ke da dukiya kusan daidai da ta sa.

Dangote ya fi samun riba ne daga kamfaninsa na Simintin Dangote, ci gaban matatar Dangote, da kuma babbar jarin sa a masana’antu daban-daban a sassan Afirka.

Masana tattalin arziki sun danganta tashin darajar dukiyarsa da fara aiki a hankali na matatar man Dangote mai sarrafa ganga 650,000 a rana — wacce ita ce mafi girma a nahiyar.

Dangote na da kashi 92.3% cikin wannan ma’adinan mai mai darajar dala biliyan 20, wanda shi ne babban ginshiƙin ƙaruwar dukiyarsa.

Haka kuma yana da kashi 86% a kamfanin Simitin Dangote, wanda ke ƙarfi ƙasashe 10 na Afirka ciki har da Nijeriya, Ghana, Senegal da Habasha, inda ke ci gaba da samun riba sakamakon ayyukan gina ababen more rayuwa.

Bayan harkar siminti da mai, Dangote na da masana’antar takin zamani mai iya samar da tan miliyan 2.8 a shekara, tare da hannun jari a kamfanin sukari na Dangote Sugar Refinery, NASCON Allied Industries, da Bankin United Bank for Africa (UBA).

Har ila yau, yana da jarin gine-gine da kadarori a birnin Legas, ciki har da gidaje da wuraren kasuwanci guda shida, waɗanda aka kimanta darajarsu ta hanyar ƙididdigar haya daga CBRE Broll Nigeria.

Sabon matakin da Dangote ya kai ya ƙara fito da sunayen Nijeriya da Afirka a taswirar arzikin duniya, yana kuma ƙarfafa hujjar cewa masu zaman kansu a nahiyar na iya taka rawa mai muhimmanci wajen haɓaka tattalin arziki.

By ukarofi