Gwamnati ta ƙara himma don kawar da gurɓatattun magunguna a ƙasar nan – Pharm. Halliru Binji

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙungiyar Masu Harhaɗa Magunguna na ƙasa kuma shugaban ƙungiyar Community Pharmacy na  jihar Sakkwato, Pharmacy Ibrahim Halliru Binji ya bayyana taron da aka yi na ƙungiyar masu harhaɗa magunguna na ƙasa PSN karo na 98 a jihar Kano da cewa komai ya tafi yadda ya kamata a taron.

Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da yan jarida a yayin taron  ƙungiyar ta masu haɗa magunguna da akayi a jihar Kano ya ce su a jihar su ta Sokoto ƙungiyar tana samun cigaba sosai da haɗin kai yanzu haka ma su 40 suka zo taron na ƙasa daga Sakkwato daga cikin su sama da100.

Da ya juya kan  lamarin gurɓatatun magaguna da ake samu a ƙasar nan yace  abu ne mara kyau mara daɗi kuma ya san Gwamnati tana mutuƙar ƙoƙari domin kawar da lamarin, amma dai yana da kyau ta ƙara himma sosai, domin akwai iyakoki da ake shigowa dasu ta ciki  ta hanyar da bata dace ba.

Pharmacy Ibrahim Halliru Binji ya ce akwai mahalarta taron da suka kai kusan 2,500 da suka zo daga faɗin ƙasar nan da jihar Kano ta karɓi baƙuncinsu da karramawa ya yi kira akan ƙarin  samun haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙungiyar a ƙasa baki ɗaya domin cimma nasara samar da magunguna ingantattu.

By ukarofi