Ƙungiyar Gwagware Network Foundation Funtua za ta raba magunguna ga yara 300 masu ɗauke da cutar ƙazuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Harwala yau ƙungiyar za ta raba wa yara 500 da akayi masu kaciya kayan sawa da zaman sun warke kaciyar.

Ya ce waɗannan yara za a zaƙulo su ne daga yankin Funtua kuma ƙungiyar har ta riga ta tanadi kayan sawa da za ta raba masu.

Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman wanda ya shaidawa manema labarai haka a Katsina ya ce bai wai yara masu cutar ƙarzuwa ba, harma da sauran cututtuka na jiki za su amfani da magani.

Ya ce tuni dai ƙungiyar ta sayi magungunan da nan bada jimawa ba za a rabawa marasa lafiyar.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa da zarar ta gama rabon magunguna ga masu cutar ƙarzuwa za ta juya wajan yaran da akayi masu kaciya.

A cewar shugaban,”wannan ƙungiyar ta Musa Adamu Gwagware Network Foundation Funtua za ta raba wannan tallafi ne ga yaran da iyayensu basu da halin kulawar da ya’yan su,”Suleiman ya ce.

Ya kuma yaba da irin matakan jin ƙai da tausaya wa da gwamna Dikko Raɗɗa ke nunawa wajen tafiyar da harkokin gwamnatin sa.

Kwamred Suleiman ya bada misali da yadda kwanan nan gwamna Dikko Raɗɗa ya rabawa manoma kaya marasa galihu a shiyar Katsina , Funtua da Daura domin karfafa masu gwiwa.

“Abubbuwa na alheri da jin ƙai ga yara marasa galihu da gwamnan ke aiwatarwa ya jawo hankalin ƙungiyar ita ma ta ce bari ta bada na ta gudunmawa,kuma za ta cigaba da irin wannan aiki na alheri,”inji Suleiman.

Kwamred Mannir wanda harwala yau shine shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua ya ce a ƙarshen wannan wata ƙungiyar Musa Adamu Gwagware network za ta buɗe ofishin ta a garin Katsina domin sauƙaƙa ayyukan ƙungiyar.

Kwanan baya ƙungiyar haɗin Funtua da kwamred Suleiman ya jagoranta suka raba tallafi na kuɗi ga marasa lafiya a Babban Asibitin Funtua.

By ukarofi