
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Gusau/Tsafe ta Jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, ya ɗauki nauyin koyar da mata sana’o’i, wanda gidauniyar Sidiya Charity Foundation za ta jagoranta.
Yayin da suka kammala karɓar horon sana’o’in, Hon. Kabiru zai ba su jari domin fara kasuwanci domin zama masu dogaro da kansu.
Kimanin mata 50 ne za su amfana da shirin koyar da sana’o’in, wanda ya dace da manufar Hon. Kabiru na tallafa wa mata da matasa, da kawo sauyi da sauƙin rayuwa ga al’ummarsa.
Wannan ba shi bane karo na farko da yake irin wannan aikin alkhairi, inda Mai Palace ya jima yana taimako da sadaka acikin al’umma, kamar yadda gidauniyar ta bayyana a wata takarda.
Gidauniyar ta kuma yi masa fatan Allah ya saka masa da alkhairi tare da ƙara masa nasara a jagorancin da yake yi domin amfanar da al’umma.
