Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Flagship College of Nursing Science da ke Bichi ta gudanar da bikin ƙaddamar da sabbin ɗalibai na wannan shekarar ranar Lahadi.
Ɗaliban da aka ƙaddamar sun haɗa da masu karatun aikin jinya da unguwar zoma, waɗanda za su ci gaba da karatunsu a wannan makaranta ta musamman da ke Bichi, Jihar Kano.
A jawabin sa na maraba, Shugaban gudanarwar makarantar, kuma wanda ya kafa ta, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa kafa makarantar ta samo asali ne daga buƙatar magance matsalar ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya a ƙasar nan. Ya ce makarantar za ta taka muhimmiyar rawa wajen cike wannan gibi ta hanyar samar da ƙwararrun ma’aikata.
Shi ma a nasa jawabin, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Bichi, Hon. (Dr) Abubakar Kabir Bichi, ya yi alƙawarin ci gaba da ɗaukar nauyin ɗaliban asalin ƙaramar hukumar Bichi domin su sami damar yin karatu a makarantar.
A nata ɓangaren, shugabar makarantar, Hajiya Manubia Muhammad Jibrin, ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da makarantar ta cimma tun bayan kafuwarta, tare da godewa Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule, da kuma Hon. Abubakar Kabir Bichi bisa tallafin da suke bai wa ɗalibai.
Taron ƙaddamar da sabbin ɗaliban ya samu halartar jama’a da dama, ciki har da wasu ‘yan majalisar tarayya daga sassan ƙasar, tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, da sauran manyan baƙi.
