An yi garkuwa da daraktocin Ma’aikatar Tsaro shida a hanyar Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An shiga firgici a yayin da ƴan bindiga suka yi awon-gaba da daraktocin Ma’aikatar Tsaro su guda shida akan hanyarsu ta zuwa Abuja daga Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamba, 2025 akan babbar hanyar Kaba zuwa Lokoja.

An gano cewa matafiyan sun ɗauko hanya ne daga Legas zuwa Abuja domin yin jarrabawar ƙarin girma, inda suka yi ciɓis da ƴan bindigan.

Al’amarin ya girgiza Ma’aikatar Tsaro da Ƙungiyar manyan ma’aikatan gwamnati na ƙasa (ASCSN), inda suka koka game da tsaro acikin ma’aikatan gwamnati da ke tafiyar aiki na dogon zango.

A wata takarda, Shugaban ASCSN, Shehu Mohammed da Sakatare Janar Joshua Apebo, sun yi alla-wadai da hakan inda suka tabbatar da cewa an fara yunƙurin ceto mutanen da aka yi garkuwan da su.

Waɗanda sacen sune “Mrs. Ngozi Ibeziakor, Mrs. C.A. Emeribe, Mrs. C. Helen Ezeakor, Mrs. C.A. Ladoye, Mrs. J.A. Onwuzurike, da Mrs. Catherine O. Essien”, waɗanda dukkan su mambobin ƙungiyar ne kuma jami’an makarantar Command Day Secondary School (CDSS) da ke Ojo, a jihar Legas.

ASCSN ta bayyana cewa Ma’aikatar Tsaron tuni ta shirya dakarun tsaro domin tabbatar da ceto mutanen.

Wani fasinja da ya samu tserewa, ya bayyana cewa maharan sun buɗe wa motar wuta, inda ganin cewa alburusan sun gaza kutsawa cikin motar, sai suka yi amfani da wasu ƙarafuna wajen farfsa ta.

By Babaji