
A ranar Talata Kabiru Tanimu Turaki, ya karɓi ragamar jagorancin PDP a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja daga hannun ɓangaren da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Da yake magana da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar, Turaki ya tabbatar da cewa ya shiga ofishinsa a hukumance, yana mai cewa wannan mataki ya kammala dukkan tsarin miƙa ragamar jagorancin jam’iyyar.
Turaki ya soki matakan wasu mambobin jam’iyyar da suka bayyana cewa an kore su a taron jam’iyya na baya-bayan nan, inda ya zarge su da kawo ’yan daba domin tada hatsaniya a wajen wani taro da aka shirya bisa ka’ida a hedkwatar jam’iyyar.
Ya kuma yi godiya ga jami’an tsaro da mambobin jam’iyyar da suka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da cewa lamarin bai rikide zuwa tashe-tashen hankula ba.
“Muna godiya ga jami’an tsaro da mambobin jam’iyyar da suka kare secretariat duk da yunƙurin kawo cikas ga taron da aka shirya bisa ka’ida”, inji shi.
Kazalika, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa da su kula da abin da ya kira ‘halayen da ba na dimukraɗiyya ba’, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa na iya raunana jam’iyyun siyasa a ƙasar.
Bayan kammala taron manema labarai, Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na PDP ya gudanar da wani zama a Gidan Gwamnan Bauchi da ke Abuja.
A wajen zaman, Gwamna Bala Mohammed da Gwamna Seyi Makinde sun yaba wa mambobin jam’iyyar da suka nuna jajircewa wajen kare martabar hedkwatar jam’iyyar.
Sun ce haɗin kan da aka gani yana da muhimmanci wajen kare tsarin dimukraɗiyya da muradun jam’iyyar a Nijeriya.
