Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Malaman da gwamnati za ta ɗauka za su koyar a makarantun firamare na karkara ne.
Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ya bayyana hakan, a yayin wani ganawa da sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi 11 da suka fito daga shiyar Katsina tare da daraktocin su, da kuma wakilan ƙungiyar Malaman Makaranta NUT.
Dr. Kabir Gafiya yayi wa sakatarorin ilimin bayani sosai akan ayyukan Gwamna Dikko Raɗɗa kan inganta harkokin ilimin bai ɗaya.
Ya ce dalilin ganawar shine yin godiya ga malaman makaranta, tare da sauran masu ruwa da tsaki akan harkokin ilimin bai ɗaya a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu, an samu gagarumar nasara a fannin ilimin bai ɗaya a jihar.
Dr Magaji ya jawo hankalin masu halartar taron cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya cimma manufofin da ta sanya a gaba ba face sai da gudunmuwar masu ruwa da tsaki, tare da sauran al’umma baki ɗaya.
Ya sanar da cewa gwamnan jihar ya amince wa hukumar SUBEB ɗaukar ƙarin sabbin malamai musamman a makarantun dake yankunan karkara, don haka ya buƙaci malamai, da sauran masu ruwa da tsaki su cigaba da baiwa gwamnati goyan baya, wajen bunƙasa harkokin ilimi a jihar baki ɗaya.
A jawaban su, shugaban ƙungiyar sakatarorin ilimi a jihar Alhaji Zaharadden Ɗanmusa, da takwaran sa shugaban ƙungiyar malamai sun yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa akan ayyukan gine-gine na makarantu da kuma samar da kayayyakin koyo da koyarwa a makarantun ƙananan hukumomin jihar.
Sun kuma yaba wa shugaban hukumar na SUBEB akan wannan hangen nesa na tattaunawa da dukkanin masu ruwa da tsaki a jihar.
An dai gudanar da irin wannan taro a shiyoyin Funtua, da Daura a ƙoƙarin hukumar na ƙara matso da jagororin ilimi kusa da hukumar.
