Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tun a farko Malam Yahaya Masussuka ya kai koke ga masarautar Katsina kan wata ƙungiyar addini da ta matsa masa kan yadda yake gudanar da wa’azi da ya saɓa wa addinin Musulunci.
Masarautar, ƙarƙashin Sarkin Katsina ta zauna da Masussuka mai da’awar ƙur’ani zalla da ƙungiyar Izala inda aka samu masalaha.
To daga baya kuma aka sake samun ƙorafi daga ƙungiyar kamar yadda Kwamishinan Yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya shaidawa wata kafar yaɗa labarai.
A cewar Kwamishinan, ganin haka gwamnatin Katsina ta kafa kwamiti da ya ƙunshi fitattun malamai da za su yi muhawara da Malam Yahaya Masussuka domin samun maslaha.
Ya ce ba wai gwamnati na shirin hana wani wa’azi ba ne “amma dole ne duk abinda zai tayar da hankali ta yi ƙoƙarin magancewa,” Dr Bala ya ce.
Shi kuwa Auwal Musa Rafsanjani na ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama kokawa yayi akan yadda ake so a musguna wa Masussuka kan ra’ayi da yake da shi da ya bambanta da na wasu malamai.
Ya bayyana cewa shi dai Masussuka ba tuhuma yake yi ba ko ta’addanci ba, domin haka dole ne a tabbatar an kare shi a bisa ra’ayinsa da yake da hujjojinsa da zai kare wanda bai taka dokar ƙasa ya yi ba ko keta dokar addini.
Don haka dole gwamnatin Katsina ta tabbatar ba a cigaba da musguna masa ba ko illatar da shi.
Shi kuwa Al’amin Isa ya siffanta Yahaya Masussuka a matsayin Maitatsine ,domin a cewarsa Maitatsine a lokacinsa bai yadda da Hadisan Manzon Allah ba.
Saboda haka ya ce a ra’ayinsa ya zo ya kare kansa idan yana da hujjojinsa ba tare da jin tsaro ba.
Sai wani shi kuma da bai faɗi sunansa ba kira ya yi ga kwamitin da zai zauna da malamin da su ji tsoron Allah su yi adalci.
Haka kuma Malam ɗanjuma Katsina ya ce ya kamata idan akwai wani mai ƙorafi akan malamin ya je kotu, a cewarsa kotu ce kawai za ta tabbatar da laifinsa ko ta hukunta shi ko kuma ta kasafta shi.
“Amma tsari irin wannan babu ruwan gwamnati a ciki,” inji Malam Danjuma.
