Kwankwaso ya gargaɗi Gwamnatin Tarayya kan yawaitar hare-hare a iyakar Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan yadda ’yan bindiga ke ci gaba da shigowa da kai hare-hare a wasu yankunan kan iyakar jihar, yana gargaɗin cewa lamarin na iya ta’azzara idan aka yi sakaci.

A makonnin baya ne wasu ’yan bindiga suka kutsa cikin ƙauyukan Tsanyawa, Shanono da Bagwai, inda suka kashe jama’a tare da yin garkuwa da wasu kafin dakarun Nijeriya su mayar da martani. Wannan mummunan yanayi, a cewar Kwankwaso, ya zama barazana ga zaman lafiya da jihar ta sha fama wajen karewa tsawon shekaru.

Da yake jawabi a bikin yaye ɗaliban jami’ar Skyline University Nigeria (SUN) karo na huɗu a Kano ranar Asabar, Kwankwaso ya ce hare-haren da ake yi a kan iyakar Katsina da Kano sun kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakin gaggawa daga gwamnatin tarayya.

Ya lissafa Tsanyawa, Shanono, Bagwai, Gwarzo da Karaye a matsayin ƙananan hukumomi da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da ke ketowa daga jihar Katsina.

Ya ce, “Kano ta daɗe tana cikin sahun jihohin da ke samun tsaro, amma waɗannan hare-hare na baya-bayan nan sun zama barazana ta gaske.”

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP a ƙasa, ya soki yarjejeniyoyin “sulhu” da wasu al’ummomin Katsina ke yi da ’yan bindiga, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta bai wa miyagu mafaka.

Ya bayyana irin waɗannan yarjejeniyoyi a matsayin ganganci da ke kawo illa ga makwabta.

A cewarsa, “Ba shi da ma’ana a ce wata ƙaramar hukuma ta rattaba hannu kan sulhu da ’yan bindiga, sannan wadannan miyagu su ketara su jefi sauran jihohi da hare-hare. Idan gwamnati ba za ta iya kare jama’a a cikin iyakarta ba, to akwai buƙatar a sake tunani.”

Tsohon gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ’yan uwa sakamakon hare-haren, kana ya jinjinawa jami’an tsaro da gwamnatin Kano bisa yadda suka shiga cikin lamarin domin kare al’umma.

Baya ga batun tsaro, Kwankwaso ya yaba wa jami’ar Skyline University bisa dagewa da inganta matsayin karatun manyan makarantu ta hanyar haɗa gogaggun malamai na gida da na ƙetare, yana mai karfafa gwiwar daliban da ake yaye wa da su kasance masu ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi, ba kawai jiran gwamnati ba.

By ukarofi