Kwamishinan Yaɗa Labarai ya halarci taron bita na limaman Juma’a a Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Waiya ya halarci taron bita na kwana ɗaya da Majalisar Limaman Masallatan Juma’a ta Jihar Kano ta shirya ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Sheikh Dr.Muhammad Nasir Adam, tare da tallafin ƙungiyar Tallafawa Musulunci ta Nusret. Taron ya gudana ne a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani da ke Kofar Mata.

A cikin jawabin sa, Kwamishinan ya yi kira ga manyan limamai da malamai masu daraja da su ƙara azama wajen ilmantar da al’umma kan ingancin gudanar da ibada, musamman a fannoni kamar tsarki, alwala da sallah muhimmam managartan sassan da ke ƙarfafa dangantaka tsakanin bawa da Ubangiji (S.W.A).

Kwamishinan ya bayyana jin daɗinsa na kasancewa cikin malamai, waɗanda ya bayyana a matsayin malamai kuma iyaye gareshi. 

Kwamared Waiya Ya Kuma roƙe su da su ci gaba da jan hankalin jama’a zuwa ga ibada da bautar Allah da ɗa’a, maimakon shiga rigingimu kan batutuwan akida da suka jima suna jawo rashin fahimta tun shekaru aru-aru.

Haka kuma, ya tabbatar wa shugabancin Majalisar Limamai ƙarƙashin Sheikh Muhammad Nasir Adam cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai za ta ci gaba da shirya tarukan bita ga limamai kamar yadda aka fara, domin samar da kusanci tsakanin gwamnati da malamai.

“Manufar irin waɗannan taruka ita ce sanar da malamai manufofin gwamnati da shirye-shiryenta, la’akari da irin rawar da suke takawa a tsakaninta da al’umma.

A wani ɓangare na taron, Majalisar Limamai tare da ƙungiyar Nusret sun karrama Kwamishinan da lambar yabo tare da miƙa masa tarin littattafan addini da ƙungiyar ta wallafa, a matsayin girmamawa bisa gudummawar sa wajen wayar da kan jama’a da goyon bayan cigaban addini.

Taron bita ya haɗa manyan limamai daga sassa daban-daban na jihar, inda ya zama wata muhimmiyar dama ta musayar ilimi, haɓaka haɗin kai, da ƙarfafa dangantaka tsakanin shugabannin addini da gwamnati domin ci gaban al’umma.

A ƙarshe, Kwamishinan ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da haɗa kan malamai domin su kasance ginshiƙai na al’umma, tare da samar da zaman lafiya, farin ciki da yalwar arziki.

By ukarofi