Daga HABU ƊAN SARKI, Jos
A yayin da ake kukan taɓarɓarewar tsaro a yankin Arewacin ƙasar nan, musamman a jihohin tsakiyar Nijeriya kamar Jihar Filato, wasu matasa mata da ke harkar tallata kayan da suke sana’antawa a zaurukan sada zumunta, sun bayyana kansu ƙarƙashin shirin kasuwar bajekoli ta Arewa, da suka yi wa laƙabi da Arewa Festival, inda masu ƙananan sana’o’i fiye da ɗari da ashirin suka samu fitar da kayan da suke sayarwa ga jama’a a babban filin Polo na Jos.
Wani abin burgewa da ƙayatarwa a taron shi ne yadda ƴan kasuwar suka fito daga ɓangarori na addini da al’adu daban-daban, kowa na ƙoƙarin neman sabbin abokan ciniki da ƙarfafa sabuwar alaƙa.
Wasu mata da wakilinmu ya zanta da su a filin kasuwar bajekolin sun bayyana farin cikinsu da samun wannan dama ta ganawa da abokan cinikin su gaba da gaba, saɓanin yadda a baya ake ciniki ta onlayin. Aisha Abdulhameed Isma’il da ke harkar sayar da turare da kayan ƙamshi ta bayyana cewa, ba kasafai wasu mutane ke yarda su tura wa wani ɗan kasuwa kuɗi a waya don su sayi kaya a wajensa idan ba su san shi ba. Amma yanzu wannan kasuwar ta bata damar samun sabbin abokan ciniki.
Hafsat Musa Ayuba, mai Hafsee Collection & More, wacce ke sayar da kayan mata na sutura, jakankuna, turare da man shafawa ita ma ta bayyana farin cikinta da Arewa Festival, saboda yadda ka samu ciniki sosai fiye da wanda take yi a gida. Ta ce, “Wannan shi ne karon farko da aka taɓa shirya kasuwar bajekoli irin haka a Jos, fatana ko da ban yi ciniki sosai ba, in haɗu da sabbin masu ciniki da za su sanni da abin da nake sayarwa, mai yiwuwa ko da nan gaba suna neman abu, za su nemi ni.”
Akwai kuma, Naanbam Miriam Shikmut da ta kai kayan abinci da ake sarrafawa ga masu lalurar ciwon suga ko kansa, da suka shafi kayan yaji, garin dankali da ake yin tuwo da shi da sauran kayan abinci na musamman. Ta yabawa masu shirya kasuwar da suka haɗa ƙananan ƴan kasuwa Musulmi da Kirista a waje ɗaya, wanda hakan ya ƙara ƙarfafa zumunci da zaman lafiya. Ta nemi gwamnati ta tallafa musu da rancen kuɗi ko tallafin jari, don su samu ƙwarin gwiwar tsayawa da ƙafafunsu, musamman ita da take buƙatar ƙananan injunan busar da kayan abinci da suke buƙatar tsafta.
A rumfar Malama Maryam Shu’aibu da ke sayar da kayan gyaran jiki na mata, musamman mayukan da ake shafawa a fatar jiki. Ta ce, duk da kasancewar ta ma’aikaciyar gwamnati hakan bai sa ta naɗe hannu ba, ta buɗe kamfanin ta na kasuwanci mai suna Mismal Glow Girls, domin taimakawa yaran mata da shawarwari kan yadda za su kula da fatar jikinsu, ta hanyar sanin nau’ikan halittar fatar su da man da ya dace su shafa, don su ƙara kyau da kula da jikinsu.
Ta ce, “Sana’a tana da matuƙar amfani ga rayuwar mace, musamman duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki. Akwai kayan sayarwa da wasu ayyuka da ake yi na samun taro da sisi, da aka bajekolinsu, kuma duk na yaran mata ne, har da kayan lalle na ƙunshi kayan ƙwalama da ruwan sanyi.”
Wani abin armashi shi ne, wata rumfa da aka baje littattafan karatu na yara ƴan makaranta, domin iyaye su riƙa koyar da yaransu a gida, musamman a wannan lokaci da aka shiga matsalar tsaro, inda har wasu jihohi suka dakatar da harkar karantarwa. Hajiya Jamila Mu’azu Abubakar ita ce shugabar makarantar Read Global Academy Jos, kuma ta ce musamman suka wallafa waɗannan littattafai don ƙarfafa gwiwar iyaye da ɗalibai akan sha’anin karatu.
Ɗaya daga cikin wakilan Arewa Festival da suka shirya wannan bajekoli a Jos, Maryam Umar ta ce, babu shakka burinsu na buɗe wannan kasuwa ya cika, don mata ƴan kasuwa sun amsa kira, kuma garin Jos ya amsa sunansa garin zaman lafiya da yawon buɗe ido.
Maryam wacce ita ce sakatariyar kwamitin tsare-tsare na Arewa Festival a Jos ta ce, kasuwar bajekolin sana’o’in mata na Arewa Festival ba an shiryata don musulmi kaɗai ba ne, sai don ƴan kasuwa Musulmi da Kirista da ke ko’ina a jihohin Arewa 19, domin su haɗa hannu su tallafawa junansu ta fuskar kasuwanci.
Wannan kasuwa ta yini biyu ta gudana ne lokaci guda da na sauran jihohin Arewa da aka shirya gudanarwa tare, an shirya ta ne a wani ɓangare na bikin Makon Ƙananan Ƴan Kasuwa na Duniya, kuma a cewar waɗanda suka jagoranci gabatar da bajekolin za su riƙa shiryawa ne duk shekara, a daidai lokaci irin wannan.
