Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An bayyana wajen da ake gudanar da Mauludi da cewa wuri ne mai matuƙar muhimmanci da ake ƙara nuna soyayya da kauna ga Manzon Allah (SAW), tare da koyon kyawawan halayensa domin samun rahamar Allah (SWA). Wannan furuci ya fito ne daga bakin fitaccen malamin addinin Musulunci na garin Dawakin Kudu, Malam Sa’idu Ahmad Gidan Nagunda, yayin Mauludin Zawiyyar Gidan Nagunda da aka gudanar a makon da ya gabata.
Malam Sa’idu ya ce Mauludi wata babbar makaranta ce da ke ƙara kusantar da al’umma ga Annabi (SAW), musamman matasa da yara. Ya bayyana cewa a nan ake koya musu kyawawan halayen Annabi, mu’amalarsa, da yadda ya jagoranci al’umma a zamaninsa. Ya ce: “Alhamdulillah, yadda yara ke karɓar Mauludi yana nuna cikakkiyar soyayya ga Ma’aiki. Wannan wuri ne da ke cusa soyayyar Manzon Allah tun daga ƙuruciya. Manzon Allah ma ya umarci iyaye su koya wa ’ya’yansu abubuwa uku, na farko shi ne son Annabi.”
Malamin ya yi kira ga iyaye da su kula da irin makarantun da suke tura ’ya’yansu, musamman makarantun addini, saboda su samu tsira da tsare imani.
Ya kuma yaba wa masu shirya Mauludin bisa jajircewarsu da kokarinsu, tare da kiran sauran al’umma da su yi koyi da irin wannan aiki domin samun dacewa.
A nasa jawabin yayin Mauludin, Shaikh Lawi Atiku Sanka ya ce hanya mafi sauki ta magance matsalolin da ake ciki ita ce ta cusa soyayyar Annabi a zukatan al’umma. Ya ce soyayyar Ma’aiki ce mafita a wannan zamani da ake fama da kalubale iri-iri.
Shi ma ɗaya daga cikin iyaye da suka halarci Mauludin, Alhaji Hussaini Isah Gidan Nagunda, ya yaba wa matasan da suka shirya taron tare da ƙara musu kwarin guiwa a irin aikace-aikacen alkhairi.
A ƙarshe, malamai da masu halarta sun ja hankalin al’umma da su ƙara jajircewa wajen nuna soyayya ga shugaban halitta Annabi Muhammadu (SAW).
