Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon bincike da Ofishin Babban Mai Duba Asusun ƙasa (OAuGF) ya gudanar ya sake jefa Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), cikin ruɗani bayan gano yawan kuɗaɗen da aka kashe ba tare da izini ko takardun shaida ba.
Wani rahoton da jaridar News Point ta wallafa ya ce, rahoton, wanda ya shafi ma’amalolin shekarar kuɗi ta 2021, ya gano matsaloli guda 28 da suka kai sama da biliyan N61.1, suna haɗe da biyan kuɗi ba tare da takardu ba, rashin bin dokokin gwamnati, ayyuka da aka bari ba a ƙarƙare ba, da kuma cin zarafin dokokin kwangila.
Rahoton ya bayyana cewa an yi biyan fiye da biliyan N30, dala miliyan 51, fam miliyan 14 da yuro miliyan 5 ba tare da cikakken bayani ko izinin da ya dace ba.
Ofishin Odita ya bayyana wannan a matsayin wata alama ta raunin tsari da rashin ingantaccen kulawa da kuɗin gwamnati, yana mai cewa duk inda takardu ko hujjoji suka ɓace, lallai a bi tsarin da ya dace ba.
Wani ɓangare da ya ɗauki hankalin jama’a shi ne na ofishin NNPCL na Landan, an ui amfani da fiye da fam miliyan 14.3 ba tare da takardar shaida ko wata shaida da ke nuna yadda aka yi amfani da kuɗin ba. An bayyana kuɗaɗen da suka shafi albarkatun ma’aikata, ayyuka na yau da kullum da sauran kashe-kashen kuɗi, amma babu duk wata shaida da za ta tabbatar da gaskiyar abin da aka yi.
Duk da cewa NNPCL ta kare kanta da cewa tana da cikakkun takardu a ofishin Landan, Odita ya ƙaryata wannan batu, yana mai cewa idan kamfanin ya gaza gabatar da su, duk kuɗin za a bi su duka.
Rahoton ya kuma zargi kamfanin da wasu manyan laifukan kuɗi a cikin gida, da suka haɗa da biyan kuɗaɗe ba tare da izini ba, rashin fitar da kuɗaɗen haraji, biyan kuɗaɗen motoci ga ma’aikata marasa cancanta, kashe kucin ayyuka da ba a aiwatar da su ba, da kuma almundahanar ƙarin kuɗaɗen ruwa lokacin da aka sauya jirgin ruwa ba tare da amincewa ba — lamarin da ya ƙara tsadar kwangilar kusan dala miliyan biyu.
Rahoton ya nuna cewa dukkan waɗannan matsalolin sun faru ne a lokacin shugabancin Mele Kyari, wanda ya jagoranci kamfanin tun 2019 kafin a cire shi a farkon shekarar 2025. Sabon GCEOn, Bayo Ojulari, ya gaji wannan gidan cike da matsalolin da ake bin bayansu har yanzu.
Rahoton ya ba da shawarar a kira shugaban kamfanin gaban kwamitocin kula da asusun gwamnati na majalisar dokoki domin ya bayyana wa ’yan ƙasa dalilin waɗannan kura-kurai.
Har ila yau, ofishin Odita ya ce duk ma’aikacin da ba zai iya gabatar da takardun shaida da bayanin yadda aka kashe kuɗi ba, a lokaci guda a ɗora masa alhakin biya.
Wannan lamari ya kuma sake hasko matsalolin da suka daɗe suna damun hukumomin gwamnati — tun daga NDDC zuwa NPA da wasu ma’aikatun tarayya — inda a kai a kai ake amfani da kuɗin gwamnati ba tare da takardu ko bin tsarin biyan kuɗi ba. A yawancin hukumomin gwamnati ana fama da ayyuka na boge, biyan kuɗi ga kwangiloli da ba su da tushe, da kuma rashin gabatar da bayanan kashe kuɗi.
Masu sharhi na cewa matsalar da ta dabaibaye NNPCL ba sabon abu ba ne, domin rahotannin Odita daga 2017 zuwa yau sun riƙa nuna ɓoyayyun kuɗaɗe da suke kai har sama da tiriliyan N2.6 da wasu miliyoyin daloli da ba su da takardun shaida. Yawancin masana sun ce wannan ya nuna cewa ba matsalar mutum ɗaya ba ce, illa wata tsohuwar matsala ta tsarin sarrafa kuɗin gwamnati da take buƙatar gyara daga tushe.
A halin yanzu, ana jiran yadda majalisar dokoki za ta karɓi rahoton da irin matakin da za ta ɗauka, yayin da jama’a da masana ke kira ga aiwatar da hukunci mai ma’ana domin maido da amincewar ’yan ƙasa kan yadda ake tafiyar da kadarorin Nijeriya.
