
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen jagoran ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa ya sako mutane 37 da aka yi garkuwa da su, waɗanda ke komarsa a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.
A cewar rahoton Zagazola Makama, ƙwararre mai sharhi kan lamuran tsaro, mutanen, waɗanda galibinsu maza da mata ne, an yi awon-gaba da su a hare-hare da aka ƙaddamar a wasu ƙauyuka, inda aka sako su a ranar Laraba bayan kwanaki da dama a hannun ƴan bindiga.
Hakan na zuwa ne bayan makonni ana tattaunawa wanda ya kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yadda ɗan majalisa Abdulraham Kandarawa ya bayyana.
Kandarawa, wanda ke wakiltar mazaɓar Bakori a majalisar dokokin jihar, ya ce sakin na baya-bayan nan ya kai jimillar adadin mutanen zuwa guda 82.
A baya ya bayyana cewa mutane 45 sun samu ƴanci a ƙarƙashin irin wannan yarjejeniyar ta zaman lafiya.
Da yake magana da manema labarai a Katsina, Kandarawa ya ce mutanen na hannun ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Sabe ta Jihar Zamfara, kuma an sako su ba tare da an biya kuɗin fansa ba, sakamakon ci-gaba da tattaunawa da ƴan bindigar, kamar yadda ATP Hausa ta wallafa.




