Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a garin Daura a cigaba da ziyarar aiki a ƙananan hukumomin jihar.
Ya ce shi ba zai taɓa juya wa al’ummar ƙaramar hukumar Daura baya saboda tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari da ya taimaka masa a zaɓen 2023.
Gwamnan ya bayyana ƙasar Daura a matsayin ƙasa mai ɗinbin tarihi ga shi ƙasa mai muhimmanci a siyasar Nijeriya.
Malam Dikko Raɗɗa wanda ke cike da farin ciki ganin yadda ɗaruruwan mutane suka fito tarbar sa, ya sha alwashin cigaba da bin aƙidar tsohon shugaban ƙasar ta nuna jagoranci bisa gaskiya da riƙon amana.
Ya yi alƙawarin ƙulla kyakkyawar haɗaka da ƙaramar hukumar Daura domin ƙarfafa dangantakar da ke tsakani na da Marigayi Muhammadu Buhari.
Raɗɗa ya ce”Na rantse da Allah tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari na da hannu a kujerar da nake zaune a kai yanzu, ya taimaka mani Allah kuma ya bani kujerar Gwamnan jihar domin haka ba zan juya wa Daura baya ba,”Dikko ya ce.
Domin haka muna tare da mutanen Daura. Muna biyayya gare su,muna mutunta su,za mu cigaba da taimaka masu a kowane lokaci,”inji Gwamnan.
Ya sanar da cewa ƙarƙashin shirin bunƙasa birane, gwamnatin jihar ta bada aikin gina tagwayen hanya mai tsawon kilomita 14.4 da zai kewaye garin Daura.
