Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP ta sace a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sojojin Operation Hadin Kai sun ceci ’yan mata 12 da ake zargin mayakan ISWAP ne suka sace a yankin Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a Jihar Borno.

An sace ’yan matan ne a ranar 23 ga Nuwamba yayin da suke aikin girbi a gonakinsu. Harin ya sanya mazauna yankin da dama tserewa zuwa makwabtan ƙauyuka.

A cewar majiyoyin tsaro da jaridar Zagazola Makama ta fannin yaki da ta’addanci ta rawaito, an gudanar da aikin ceton ne a ranar Asabar. Har yanzu ba a tabbatar ko an biya kuɗin fansa ba.

An ‘yan matan wani sansanin soja domin duba lafiyarsu da karbar bayanan su kafin a mayar da su ga iyalansu.

A makonnin baya-bayan nan, arewacin Nijeriya na fama da ƙaruwa a hare-haren tarzoma da garkuwa da mutane, ciki har da harin kwanton bauna da ISWAP ta kai wa jerin gwanon sojoji a Borno, wanda ya yi sanadin kama Brigadiya Janar M. Uba, daga bisani aka kashe shi.

A jihohin Zamfara, Sokoto da Yobe ma an ci gaba da samun garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Fiye da ɗalibai 200 aka yi garkuwa da su a jihohin Neja da Kebbi, yayin da aka sace masu ibada 38 a wani coci a Kwara.

By ukarofi