Yadda wata tsohuwa ta sauke Alƙur’ani a Argungu 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Karshen makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye ɗalibai a ɗaya daga cikin makarantun da ke ƙarkashin kulawar ƙungiyar Mar’atussaliha Widows and Orphans Initiatiɓe reshen ƙaramar Hukumar Argungu da ke jihar Kebbi.

Sai dai abinda ya fi ɗaukar hankali a wajen bikin yaye ɗaliban shi ne, daga cikin ɗaliban akwai Malama Habiba Saidu wata tsohuwa mai kimanin shekaru saba’in da ita ma tana daga cikinsu.

Da ta ke zantawa da wakilin Blueprint Manhaja Malama Habiba Saidu ta gode wa Allah da ya ba ta ikon sauke Alƙur’ani mai girma da ta dade tana burin samun haka.

Ta bayyana cewa ta dade tana burin sauke Alƙur’ani ta taba karatu a wajen wata malama Rukayya bayan raauwar mijin ta sai ta dawo gida daga nan sai kuma ta sake aure a wannan anguwar ta Allugu duk da ya ke ba ta taba haifuwa ba, tana nan zaune da sabon mijin ta shi ma Allah ya yi masa rasuwa, amma ganin irin hidimar da da ta yi wa mijin sai yayan sa suka ce ba za tafi ko ina ba saboda yanzu ita ce mahaifiyar su, suna nan zaune a haka tare da yayan mijin ta sai Allah ya sa aka bude wannan makarantar daman tana da wannan burin saboda haka sai ta yanke shawarar komawa makaranta don ta cigaba da karatu da ya ke ba ta sami sauke Alƙur’ani ba a lokacin kuruciya.

Ta ƙara da cewa ba nan za ta tsaya ba in sha Allahu za ta cigaba da karatu har zuwa abinda hali ya yi saboda yanzu haka ta sauke Ahlari da Ishmawi kuma tana karatun Hadisi.

Ta ce a bangaren mu’amala kuma tana da dangantaka mai kyau tsakanin ta da malaman ta da suka haɗa da Malama Shinko da Malama Amina saboda huldar su tamkar ta Kaka da Jika ce ko a cikin karatu wannan ya taimaka mata kwarai wajen fahimtar karatu.

Ta yi kira musamman ga mata da su tashi tsaye su dage wajen neman ilmi don gyaran ibadar su domin samun tsira gobe lahira, ko da ba su iya karatu yana da kyau su rinka zuwa makaranta suna sauraron wa’azi.

Malama Mariya yi A. Bawa Allugu ita ce malamar da ke koyarwa a makarantar ta kuma bayyana wa wakilin mu da cewa ta godewa Allah da ya saka ta a hanyar koyarda fannin addinin musulunci.

Ta bayyana Malama Habiba a matsayin jajirtacciyar mace saboda ba kasafai a ke samun tsofaffi masu irin shekarun ta ba da ke iya jajircewa su koma makaranta suna karatu ba har kuma bayan sun sauke Alƙur’ani kuma su cigaba da karatun sauran littattafai ba.

Ta shawarci mata musamman tsofaffi da su dawo makaranta su cigaba da karatu saboda shi karatu ba shi da makara musamman wadanda ba su yi karatun ba har ma da wadanda suka yi su zo su cigaba saboda akwai fanni daban-daban tun kama daga na kananan yara har zuwa manya saboda neman ilmi wajibi ne ga kowane musulmi.

Ta kuma yi addu’ar Allah ya saka wa wanda ya assasa wannan makarantar tare da duk wadanda ke bayarda gudummawa don cigaban ta da alkhairi.

Malama Habiba Saidu ta sami kyautuka daban-daban bayan kyautar game-gari da aka baiwa daliban da suka suka.

Shugabar ƙungiyar Hajiya Mariya Muhammad Mera tare da Uwargidan tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Murjanatu Bello Dantani Magajin Rafin Kabi sun jinjinawa Malama Habiba Saidu bisa ga jajircewar da ta yi har sai da ta cimma burin ta na sauke Alku’ani mai girma.

A cikin jawaban su duka sun yi kira ga mata jami’an da su tashi tsaye su dage wajen neman ilmi na addini da nazamani tare da neman sana’o’i

By ukarofi