Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a ƙaramar hukumar Kaita lokacin da ya kai ziyarar aiki a yankin.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ware wannan kuɗi a cikin kasafin kuɗin ƙasa na 2026 domin kammala aikin madatsar ruwan na Kaita da aikin ya tsaya cak.
Gwamna Raɗɗa ya ce wannan tallafi babban ci gaba ne ga al’ummar yankin da suka shafe shekaru suna jiran farfaɗo da aikin da aka bari kuma da zaran an kammala aikin zai taimaka wa manoman noman rani ,ya kuma samar da wadataccen ruwan sha a ƙaramar hukumar ta kaita.
Ya kuma nanata ƙudirin gwamnatin jihar na tabbatar da adalci, gaskiya, wajan biyan diyya ta gaskiya ga duk masu gonaki da aikin zai shafa, musamman manoma da filayen su ke cikin yankin aikin madatsar ruwan.
“Madatsar Ruwan Kaita ginshiƙi ce ta rayuwar manoman rani da al’ummar karamar hukumar kaita,”Inji Dikko Raɗɗa.
A yayin ziyarar, Gwamna Raɗɗa ya kuma tabo tsofaffin buƙatu na gina hanyoyin Dutsin Safe zuwa Riko,Kagadama da Babbar Ruga,Matsai.
Ya ce waɗannan hanyoyi biyu muhimmai ne ga zirga-zirga, noma da harkokin kasuwanci, tare da nanata cewa inganta hanyoyin karkara na daga cikin ginshiƙan shirinsa na bunƙasa tattalin arziki.
Yayin wani taron masu ruwa da tsaki, gwamnan ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Kaita bisa ƙaddamar da shirin tallafawa jama’a mai faɗi wanda aka yi niyya ga mata, matasa, mabuƙata, da ɗaliban makarantun gaba da sakandare.
Ya ce wannan shiri ya dace da ƙudirin gwamnatin jiha na rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Kayayyakin tallafin da aka raba sun haɗa da injinan nika 100, injinan dinki 100, injinan nika barkono 100 don tallafa wa sana’o’in gida da ƙananan ‘yan kasuwa a yankin.
Sauran kayan tallafin sun haɗa da kwanonan masu yankan nama 150, tallafin jari na ₦50,000 ga masu yankan nama 50, injinan amfani da hasken rana na tara ruwa 50, da shirin bayar da tallafin kuɗi Naira 45 miliyan ga matasa mabukata da masu ƙananan sana’o’i su 600.
Ƙaramar hukumar ta kuma samar da motoci Peugeot bakwai da Toyota Corolla uku don aiki, babura 40 don ayyukan ofis, tare da tallafin karatu na naira miliyan 15 ga ɗalibai 540 na makarantun gaba da sakandare daga yankin.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana waɗannan ayyuka da cewa “shaida ce ta jagoranci mai karkata ga bunƙasar ƙananan hukumomi.”
Tun da farko, yayin tarbar gwamnan, Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin Kaita, Alhaji Yazid Abdulmumini Kabir, ya roƙi a ci gaba da matsa lamba domin tabbatar da gwamnatin tarayya ta kammala aikin madatsar ruwan, yana mai cewa shi ne aikin da ya fi muhimmanci ga manoman yankin.
