
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jagorancin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ya amince da buƙatar Gwamnan Tarayya ta janyewa daga yin zanga-zangar rashin tsaro da wasu al’amura na tsare-tsaren tattali.
An cimma yarjejeniyar ne bayan ganawa da Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda ya jagoranci tawagar jagororin NLC zuwa wajen Shugaba Bola Tinubu a daren Talata.
Bayan cigaba da zaman ne a yau Laraba, Gwamna Uzodimma da Shugaban NLC Joe Ajaero suka gana da manema labarai.
Uzodimma ya ce, tsoma baki da Tinubu ya yi ya taimaka matuƙa wajen warware matsalolin, sannan an buɗe fagen tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago.
Ajaero a nasa jawabin, ya ce ɓangarensa ya amince da alƙawuran da gwamnatin tarayya ta yi, waɗanda za a yi nazari a kansu tare da aiwatar da su nan da wani ɗan lokaci.
Ana samun rahotannin hare-haren ƴan ta’adda a garuruwa, cocina da masallatai a sassan Nijeriya musamman daga wata guda zuwa yanzu, lamarin da ya sa Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin tsaro.
