Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Malam Muhammad Rabi’u shugaban masu sana’ar sayar da jaridu ta ƙasa (Vendors )reshen jihar Katsina ya yi wannan kira a wata takardar sanarwa da ya fitar.
Ya ce ƙungiyar ta fi shekara 30 da kafuwa amma basu taɓa samun tallafi daga gwamnatin jihar ba.
Malam Rabi’u ya bayyana cewa da kafuwar ƙungiyar,ta na da mambobi fiye da arba’in “Amma yanzu mutum shida suka rage,”Inji shi.
“Mai da gidajen jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai a yanar gizo da matakin gwamnati na tsayar da sayen jaridu ya taimaka wajen durƙushewar sana’ar mu,”Inji Malam Rabi’u.
Shugaban ƙungiyar ya nuna damuwarsa da a shekarun baya duk ma’aikatun gwamnati da ofishin gwamna da mataimakin sa a duk rana suna sayen kwafi,amma yanzu,sun ƙauracewa saye inji shi.
Domin haka yayi kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya shiga lamarin su ko sa farfaɗo da halin ƙunci rayuwa da suka shiga sakamakon rashin aikin yi.
“Ina kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya duba cikin irin tallafawa da yake wa ƙungiyoyi,ya duba ta mu ƙungiyar domin mu nemi wata sana’a.
