An sake saya wa unguwannin ƙaramar hukumar Bichi bututun ruwan famfo

Spread the love

An yi kira ga al’umar Bichi su rika bijiro da bukatun ayyuka da suke da bukata ga Majalisar karamar hukumar, domin inganta al’amuran rayuwarsu.

A wata sanarwa da Jami’ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya yi wannan kiran ne a yayin kaddamar da bututun ruwa ga wasu unguwannin karamar hukumar a ofishinsa dake sakatariyar Bichi, inda ya bayana farin cikinsa na aiwatar da wannan aiki da ya yi a karamar hukumar.

“Kamar yadda kansilan harkar ruwa ya fada, wannan kusan shi ne kashi na biyar da muka raba wa ungiwanni fayib-fayib, sannan su kansu mutanen wadannan unguwanni mun gode musu kwarai da gaske, domin tun da suka roki a samar msu wadannan fayib din suka jure, wasu sai ka ga sun karaya ya ga kamar ba za a ba shi ba, amma su kullum sai dai addu’a da fatan alheri da kuma cewa suna tuni. Katsan Allah cikin ikonsa yanzu ga shi cikin kwana uku Allah ya yanke mana, unguwanni shida ne, muka fara diban wasu daga ciki mu yi, su ma ragowar idan suka gani za su san cewa na su na tafe.” In ji shi.

Shugaban Sashen Tsaftar Muhalli da Ruwa na karamar hukumar, Malam Ibrahim Haruna, da ya samu wakilcin Malam Kabiru Bello, ya yaba wa shugaban yankin bisa kokarin samar da manyan fayib din isar da ruwa ga wasu unguwannin yankin, duba da muhimmacin ruwa ga rayuwar al’umma.

“Muna godiya Shugaban karamar hukuma, da samar da wadannan manya-manyan fayib masu mita shida kowane daya, kuma unguwannin da za su amfana; akwai hagagawa, da za su samu kimanin mita dsri hudu da ashirin 420, Hayin Waya su ma za su samu na kimanin wanban mita, unguwar Kanawa za su samu mita dari da ashirin 120.” In ji shi.

Da yake jawabi, Kansilan Tsaftar Muhalli da Ruwa, Malam Nura Abdu ‘Yan Bundu, a madadin Daraktan Mulki na yankin, Alhaji Abba Muhammad Diso, ya ce, wannan ba shi ne karon farko ba, inda a baya karamar hukumar ta share wa mutane da yawa matsalolin rashin ruwa a unguwanninsu.

“Mun shiga lungu da sako na Karamar Hukumar Bichi, musamman mazabu goma 10 da suke wajen Bichi, dukkansu inda ruwan famfo yake mun je mun sa musu fayib domin kauda matsalar ruwa a guraren, inda kuma suke da tuka-tuka suka tsaya tsawon shekaru mun je mun gyara musu, a kalla a karon farko mun gyara bohol sama da daribda hamsin 150, a karo na biyu kuma guda hamsin 50, haka a wasu mazabu a kalla mun gyara musu guda sittin 60.”

By Babaji