EFCC ta kama bokaye da dalar jabu ta miliyan 3.4

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta sanar da kama wasu mutane biyar da ake zargi ‘bokaye’ ne, tare da kwato manyan kuɗaɗen waje na jabu da suka kai dalar Amurka 3,430,000 da kuma Yuro 280,000, a jihohin Osun da Legas.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, an ce jami’an sashen Ibadan na EFCC sun kama mutanen ne a ranakun 7 da 8 ga Disamba, 2025, bayan bin diddigi da tattara bayanan sirri kan ayyukansu.

Binciken farko ya nuna cewa mutanen na yaudarar jama’a ne da sunan yi musu “asirin kuɗi” da kuma magance matsaloli iri-iri, inda suke kwace kuɗaɗen su a matsayin sadaka ko hadaya.

Haka kuma, ana zargin su da yaudarar mutane da iƙirarin cewa suna iya samar da kuɗaɗen waje ta hanyar aljanu, inda ake buƙatar a “wanke” kuɗin ta wata hadaya kafin a iya amfani da shi.

A cewar EFCC, mutanen na amfani da dabarar tsabbu wajen sa wa wadanda suka yaudara su bada kuɗaɗe domin yin abin da suka kira hadaya. Daga baya, an gano cewa dukkan kuɗaɗen waje da aka kwato jabu ne.

Baya ga kuɗaɗen, jami’an EFCC sun kuma kwato motoci biyu masu tsada da wayoyin salula daga hannun waɗanda ake zargin. Hukumar ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

EFCC ta sake jaddada gargaɗi ga ‘yan ƙasa da su guji fadawa tarkon masu yaudarar jama’a da sunan bokanci, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abu mai kama da zamba ga hukumomin tsaro.

By ukarofi