Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Zagin Shehu Mujaddadi na kan gaba cikin alamun muguwar kwangilar makirci ta ‘yan ƙaryar Hausa zalla. Hikimar zagin Shehu ita ce rushe jigo a tarihin hidima ga musulunci a wannan yankin na mu. Ko sau ɗaya ba za ka ga miyagun nan na maganar mai ya sa Bature ya kawo addininin Kirista har wasu daga masu bautar GIJI su ka shiga addinin su ka nemi yi wa GIJI da gizagizai kishiya ba. Ba za ka taɓa ji ko gani sun soki lamirin Turawa da su ka riƙa jidar ƙarfafan mutanen Afurka ta yamma zuwa aikin gonakin reke a Amurka daure da sarka a matsayin bayi ba. Ba sa korafi kan kwashe dukiya da kayan tarihinmu da Turawa su ka yi.
Abu na biyu duk da ‘yan farafaganda sun gaza samun nasara tun ɗaure Nnamdi Kanu, sun cigaba da jinjinawa Chukwua Nzegwu wanda ya sa bindiga ya harbe Firminiya Sir Ahmadu Bello da matarsa. Mai yabawa wanda ya kashe Sardauna a matsayin jarumi tabbas maƙiyin al’ummar Arewacin Arewa ne kuma maƙiyin ma;abota son zaman lafiya a Nijeriya ne. Ba a je ko ina ba sai mutanen su ka fito da ajandarsu ta mara baya ga wasu tsirarun ‘yan siyasa masu bahaguwar manufa na Arewa ta tsakiya da su ka ƙirƙiro sunan MIDDLE BELT. Na sa mu ku inda su ke cewa su na mara baya, MIDDLE BELT su fice daga Arewa. Asalin dalilin MIDDLE BELT shi ne kin jinin hatta alaƙanta yankin da Arewa don su a ganinsu sunan Arewa na Hausawa ne kuma ma’anarsa ta biyu addini!. Ban da Maguzawa da ke rakuɓe a Arewacin Arewa, gaggan ‘yan ƙaryar Hausa zalla ‘yan kananan ƙabilun wannan yankin ne da makiya Arewa su ka ƙirƙira.
Mun sha haska Hausawan bogi da su ka fito daga Arewa ta tsakiya da su ne kan gaba wajen mara baya ga Bishop Wilfred daga Binuwai, wanda ya kai ƙara don neman Amurka ta kawo hare-hare Nijeriya da nuna a na yi wa mabiya addinin Kirista kisan kare dangi. Yau da gaskiya ta yi halinta har wakilan Amurka su ka shigo Nijeriya sai tsit ka ke ji har sunan Wilfred na neman zama tarihi. Duk masu dogon baki da ke fatar ganin Amurka ta auna masallatan Jumma’a ta kawo hare-hare ko rutsawa da wasu ‘yan kauyukanmu su na wani taro kamar hatsarin da ya faru kan masu Maulidi a Tudun Biri; sun ji kunya kuma sun shiga bakin ciki don mugun nufinsu ya ci tura. Ai kun ga ba su fadawa Amurka kisan da su ka yi a Gwanin Gora da Zangon Kataf ba.
Ga uku daga cikin manyan muradun ‘yan karyar Hausa zalla:
1.Tada fitinar yakin kabilanci tsakanin Musulmi a kokuwar Arewa don ƙarfafa makircin MIDDLE BELT da tallafawa IPOB da ‘yan ta’addansu ESN su ayyana kafa Biyafara.
2.Shiga rigar Hausawa don zuga Bahaushe ya dauka akwai wani musulunci daban da na Shehu Mujaddadi don haka ba lallai ya damu da zuwa masallaci ya yi sallah ba don wai limaman mabiya Mujaddadi ne. Nuna Kabila ta fi addini na daga hanyoyin yaƙi da riƙo da Musulunci na Hausawa.
3.Rage ƙarfin faɗa ajin Arewa a siyasance don ya zama za a iya yi wa manyan ‘yan siyasar Lardin sharri da cewa ‘yan ƙabila kaza ne don haka kar a zaɓe su. Hakan tabbas zai iya dora maƙiya ƙarfin Arewa a kan madafu da za su iya wargaza Nijeriya gaba daya ta hanyar ware masu bin addini daban sauran mutane daban. Akwai wani ɗan karyar Hausa zalla da ya taba alwashin za a iya neman masu haƙiƙancewa kan addini a rasa a Arewa.
Ko gabanin na yi bincike kan miyagun mutane da ke iƙirarin karya na Hausa zalla, na fahimci sun raina Hausa da Hausawa tun da ai ba harshensu ba ne kuma ci gaban Hausawa ba damuwarsu ba ce. Kamar yanda masu hikima ke cewa in ka na son gane kowaye mutum to dubi waye abokinsa. Daga yanayin hotunan karya da zayyane-zayyane da miyagun ke kwatanta Bahaushe da su za ka gane irin mummunan hoton Hausawa da ke zuciyarsu.
Kowa ya duba zai ga kusan duk masu ruruta fitinar nan ta ƙabilanci ba hotonsu, ba sunan gaskiya ba adireshi. Mutum na zaune a Zangon Kataf jihar Kaduna zai rubuta ya na Gwadabawa a jihar Sokoto. Wani na Mangu a jihar Filato sai ya rubuta ya na Babura a jihar Jigawa ko Batagarawa a jihar Katsina. Mutum na zaune a Sabon Tasha jihar Kaduna zai rubuta ya na zaune a Shinkafi da ke jihar Zamfara. Suna kuma duk wanda ka ga ya rubuta shi ALHAWSAWI ne ko Bahaushe waye-waye to tantirin makiyin Hausawa ne don zai iya zama Emos Kaza, Damuna A na ruwa da sauransu. Wallahi duk ranar da mutanen nan su ka yi zuciya su ka fito da kan su, magana ta kare ko kadangare na Bokkos a Filato ba zai saye su sisin kobo ba.
Zayyane-zayyane kuma daga wata mata ta na tikar rawa wasu ‘yan iskan gari su na yi ma ta kida, sai mace tsirara, sai wani na busa kamar baubawan burmi, sai wani ya daga hannu duk ya fusata kamar zindiki ya ji kiran sallah. Kai hoton Hausawa a zuciyar mutanen nan ya yi muni.
Haƙiƙa yanda miyagun nan ke ɗaukar al’adar Bahaushe cewa shagali ce ta rawa da waƙa da sharholia zai tabbatar ma na waɗannan mutane ba Hausawa ba ne, hasalima yaƙi su ke yi da Hausawa da rigar karya ta Hausawa don kona kasar Hausa ala bashi su kafa ƙasar su ta MIDDLE BELT can kuma BIYAFARA su yi dabdala a Enugu. Rasar kunyar mutanen nan ta kai furta wai ba laifin da IPOB su ka yi wa Hausawa ko Arewa. Wani mugun yaro a cikinsu ma cewa ya yi bai san kisan gilla da mutan Gwanin Gora su ka yi ta yi ba, bai san kisan kare dangi da a ka yi wa jama’a a Zangon Kataf ba. Yanka matafiya a jihar Filato ma duk a wajensa shaci-fadi ne. Wani ma da ya yi mankas da kunu sai ya ce ‘yan Arewa munafukai ne sun ki magana kan ‘yan bindiga sun koma magana kan maharba da a ka kashe a jihar Edo! Shi a wajensa kar a yi magana kan kashe-kashe na Filato, kudancin Kaduna da Edo a koma batun ‘yan bindiga kadai na Arewa maso yamma. A fili ya nuna duk inda a ke kisan nan, garuruwan ‘yan Hausa zalla ne da yankinsu na ƙirƙira wato MIDDLE BELT. Mun haska wani dan Eggon wato Alago da ke jihar Nasarawa da ke aikin Hausa zalla.
Ta hanyoyin daban-daban mun haska mutanen nan ba Hausawa ba ne kuma makiya zaman salama ne kazalika masoya IPOB ne. Zan haska wasu da har wa’azi su ke yi da sunan Musulunci, amma shuka su a ka yi don su kunna wutar fitinar yaki tsakanin Musulmi a Arewa.
Kamar yanda mu ka yi watsi da makiya Arewa da Nijeriya su Ouba Ali Mohaman na Kamaru, Kayode Salman Banjo da ‘yan IPOB da ke fesa fetur kan ciyayin a jinkar Arewa; mu na godiya ga Allah da ya hutar da mu don miyagun nan da kan su, su ke tonawa kan su asiri, kuma dubunsu na gab da cika yayin da jami’an tsaro ke bincike kan su. Duk wani ALHAWASAWI da a ka cafke a maboyarsa kar ya ce ba mu gargaɗe shi ba.
Ya zama wajibi mu haska miyagun mutanen nan ‘yan iƙirarin Hausa zalla don sauran matasa da wadanda labari tukun bai je mu su ba, su gane su don kar su fada tarkonsu. Yayin da su ke aibata duk wani mai mutunci a Arewa, a lokaci guda ‘yan Hausa zalla na yabawa su Nnamdi Kanu da tantirin dan yunƙurin juyin mulki Gideon Orkar daga jihar Binuwai jihar su Bishop Wilfred mai Amurkawa. A shafukansu na yayata MIDDLE BELT su kan fito da sunayensu na gaskiya su zagi musulmi da Hausawa. Idan sun fito a munafukai da rigar Hausawa, su kan ruruta fitinar yin yaƙin ƙabilanci tsakanin Musulmi don tabbas a dai Arewa an san su waye kan gaba wajen yawa a addini kuma addinin ya barranta da ƙabilanci. Hausawa da Fulani su ne ke tsayin daka wajen lamuran musulunci a Arewacin Arewa kuma a tsawon tarihi a na zaune lafiya da mabiya addinin kirista, don haka miyagun nan su ka zaɓi ɗinka rigar Hausawa don zuga Musulmi su aukawa juna daga manyan masallatai zuwa kasuwanni a manyan biranen Arewa.
Mu na ƙara godewa Allah da jama’a har kullum ke gane muguntar mutanen nan da yin wancakali da su. Sun zama jemagu don tabbas ko Biyafara a ka kafa ba za su samu gurbi ba inda a lokaci guda wadanda su ke yaka a Arewa ba za su iya nasara a kan su ba kuma ko an kara mu su shekara 1000 su na ƙulla wannan makircin. Ai ‘yar manuniya ta nuna a baya. Menene ba su yi ba don korar Hausawa a fitinar Filato, Binuwai da kudancin Kaduna. Har mitin su kan yi fa cewa in sun kashe waɗanda su ke ganin baki ne, ga yanda za su raba gidaje da motocin mutanen! Kai Bahaushen bogi ka na da wayo amma ba ka da hankali.
KAMMALAWA
Haba ta yaya ma Bahaushe zai zagi Shehu Mujaddadi? Sam zagi ba tarbiyyarmu ba ne. Ba yankin da ya tsolewa makiran duniya ido irin Arewa. Sun yi iya yi tun zamanin mulkin mallaka su sauyawa Lardin akala da alƙibla daga gabar zuwa yamma amma abun ya gagara. Dubban mutane da kan taru a masallatan Jumma’a da filayen idi kan konawa miyagun nan rai. A nan tsakiyar Arewa ba an taba kai farmaki kan masu sallar idi ba da nufin hallaka su gaba daya amma Allah cikin ikonsa ya aiko taimako ta inda jama’a ba su yi tsammani ba. Ko gobe su ka sake gwadawa Allah ubangijin ka’aba na nan kuma DAIRAL ABAABIIL na nan daram. Makircin zai kare kan boyayyun masu farafaganda a wayar salula yaran kartagi uban ‘yan kwangilar rusa Arewa Ouba Ali Mohaman. Mugu na Kamaru ya na yakar Ambazonia amma ya na cillo wuta don wargaza Nijeriya. Ina maimaitawa miyagun nan gara ku yi watsi da kwangilar nan don kuɗin jini ku ke ci, sam ba za ku yi nasara ba kuma in kun bijire za ku dandana kudarku tun a nan duniya balle ranar gobe kiyama.
