Kirsimeti: Zan tabbatar da ’yancin addini a Nijeriya – Tinubu

Spread the love


Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Tarayyar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta kare ’yancin yin addini da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban a Nijeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin saƙon fatan alheri na Kirsimeti na shekarar 2025 da ya aike wa ’yan ƙasar, musamman al’ummar Kirista.
A cewarsa, gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da hulɗa da shugabannin addinai domin ƙarfafa haɗin kai, daƙile rikice-rikice da kuma bunƙasa zaman tare cikin lumana.
Tinubu ya ce, a tsawon shekarar, ya yi mu’amala da manyan shugabannin addinai biyu na ƙasar, musamman dangane da damuwar da ake nunawa kan nuna rashin daidaiton addini da matsalar tsaro.
Ya bayyana cewa, za a ci gaba da irin waɗannan tattaunawa domin ƙarƙafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da cibiyoyin addini, tare da hana tashe-tashen hankula da kuma ƙarfafa zaman lafiya a faɗin ƙasa.
Shugaban ya taya Kiristoci a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Kirsimeti, yana mai cewa wannan lokaci ne na tunawa da haihuwar Annabi Isa Almasihu da saƙonsa na zaman lafiya.
Tinubu ya jaddada cewa Kirsimeti ya wuce shagali kawai, yana tunatar da bil’adama rawar da Almasihu ya taka a matsayin Sarkin Zaman Lafiya.
Ya kuma gode wa Allah da damar da Ya ba shi na yi wa ƙasa hidima a matsayin Shugaban ƙasa, tare da yin addu’ar zaman lafiya a faɗin Nijeriya, musamman a tsakanin al’umma masu mabambantan aƙidu.
Shugaban ya ce, gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙoƙin ’yan ƙasa na yin addininsu ba tare da tsoro ba, yana mai nanata cewa babu wanda ya kamata a cutar ko a gallaza masa saboda aƙidarsa ko addininsa.
A cewarsa, kowa yana da ’yancin rayuwa, ibada da bin burinsa cikin tsaro da mutunci, ba tare da la’akari da ƙabila ko aƙida ba.
Tinubu ya yaba da gudunmawar da Kiristoci ke bayarwa wajen gina ƙasa, yana cewa darussan soyayya da tausayi na Kiristanci sun zaburar da mutane da dama wajen kula da marasa galihu da kuma inganta zaman lafiya da juriya a cikin al’umma.
Ya ce ana girmama duk waɗanda ke aiki tuƙuru domin bunƙasa zaman lafiya, jituwa da haƙuri a cikin al’ummominsu, bisa koyarwar Almasihu.
Ya sake jaddada cewa tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, gwamnatinsa ke ci gaba da tabbatar wa ’yan Nijeriya aniyar kare hadin kan ƙasa da kwanciyar hankali. Shugaban ya kuma yi kira ga ’yan ƙasa da ke yin tafiye-tafiye a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara da su yi haƙuri da kiyaye doka a kan hanyoyi, yana masu yi musu fatan tafiya lafiya da dawowa gida cikin salama.
A ƙarshe, Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa kan makomar Nijeriya, yana cewa da dogaro ga nufin Ubangiji da haɗin kan ’yan ƙasa, Nijeriya za ta ci gaba da gina ƙasa mai girma wadda al’umma masu zuwa za su yi alfahari da ita.

By ukarofi