Kano: Danƙwairo ya yaba wa Gwamna Yusuf kan samar da rundunar tsaro ta jiha

Spread the love


Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano


An yaba da irin ƙoƙari da matakan da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke ɗauka domin tabbatar da ingantaccen tsaro a faɗin jihar.
Wannan yabo ya fito ne daga bakin Alhaji Muhammad Hussaini ɗankwairo (Mashƙur) Gwangwazo, jim kaɗan bayan ƙaddamar da rundunar tsaro ta Jihar Kano, inda ya bayyana matakin a matsayin kyakkyawan tunani da hangen nesa na shugabanci.
Alhaji ɗankwairo ya ce ƙirƙirar rundunar tsaro a matakin jiha wata babbar nasara ce da za ta taimaka matuƙa wajen ƙarfafa harkokin tsaro, tare da rage barazanar da ake fuskanta a wasu sassan jihar.
Ya ƙara da cewa wannan runduna ba Kano kaɗai za ta amfana da ita ba, har ma da jihohin maƙwabta, inda ya ce hakan zai zaburar da jihohin Arewa su haɗa kai domin tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
ɗankwairo ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano za su taka, ta hanyar ba da cikakken kulawa da tallafi ga jami’an tsaron cikin gida, tare da ƙarfafa al’umma su ba su haɗin kai domin su gudanar da ayyukansu cikin nasara.
Ya ce tun bayan rantsar da Gwamna Abba Kabir Yusuf, jihar Kano ke samun cigaba a fannoni daban-daban, ciki har da inganta harkokin ilimi da lafiya, gina hanyoyi, bunƙasa cigaban mata da matasa, biyan haƙƙin ’yan fansho da na kansiloli, da sauran muhimman fannoni.
A ƙarshe, Alhaji Muhammad Hussaini Dankwairo (Mashƙur) Gwangwazo ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka ne suka sa al’ummar Kano ke nuna wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ƙauna da cikakken goyon baya, tare da yi masa fatan samun nasarar kammala wa’adinsa da kuma sake samun damar yin zango na biyu.

By ukarofi