INEC ta soke PDP a jaddawalin ƴan takarar gwamnan Ekiti kan shari’o’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar jaddawalin ƴan takarar gwamnan Jihar Ekiti da mataimakansu yayin shirye-shiryen zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Yuni, 2026, inda aka ga babu suna babbar jam’iyyar adama (PDP) a ciki.

An ga cewa babu sunan ɗan takarar PDP, Dakta Wole Oluyede, da mataimakinsa, inda ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar daga jam’iyyu 12 da za su fafata a kujerar gwamnan jihar a ofishinta da ke titin New Iyin Road, Ado-Ekiti, ranar Litinin.

Jerin sunayen ya nuna cewa jam’iyyar APC na sake tsayar da gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, tare da Monisade Afuye a matsayin mataimakiyarsa.

Sauran ƴan takarar sun haɗa da Opeyemi Falegan na Accord Party, tare da Omoyemi Olaleye; Akande Oluwasegun na ACC da abokinsa Oluwasanmi Fajuyigbe; da kuma Ayodeji Ojo na ADP tare da Itunu Ibitoye.

Kazalika, ADC ta tsayar da Oluwadare Bejide da Paul Olowoyeye, yayin da APP ke da Bidemi Awogbemi da Akinyemi Adewumi a takararta.

Ana ganin rashin ganin PDP a jerin sunayen na iya kasancewa saboda rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar a mataki na ƙasa ina ake cigaba da gudanar da shari’o’i akansu.

By Babaji