
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar NNPP a Kano, ta yi watsi da ikirarin cewa wasu daga cikin mambobinta na shirin ficewa daga jam’iyyar da nufin sauya sheƙa zuwa APC mai mulki, tana mai cewa babu goyon baya akan haka a matakin jihar ko jagorancinta na ƙasa.
Shugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin a Kano, ya ce kan ƴaƴan jam’iyyar har yanzu a haɗe yake wajen cimma manufofinsu na siyasa a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya.
Ya bayyana cewa, jam’iyyar ta mayar da hankali wajen shugabancin damawa da jama’a musamman wajen bai wa ilimi, noma da inganta harkokin tattali muhimmanci a dukkan sassan jihar.
Ya kuma roƙi mambobin nasu da ke shirin barin NNPP da su sauya matsaya, yana mai kira a gare da su cigaba da zama masu biyayya ga abin da ya kira da “jam’iyya da aka gina akan adalci ga al’umma da ci-gabansu”.
Kazalika, Dungurawa ya ƙaryata batun cewa akwai rarrabuwar kai acikin jam’iyyar, musamman zarge-zargen cewa wasu mambobi na ƙoƙarin haddasa rikici tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar da Jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cewarsa, rahotannin ba gaskiya ba ne, abu ne aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a da kuma ƙoƙarin haifar da tsaiko ga haɗin kan da ke cikinta.
