An samu zaman lafiya a Katsina, inji Gwamna Raɗɗa 

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina 

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya tabbatar wa mazauna jihar gagarumin ƙudIrin gwamnatinsa na samar da shugabanci mai inganci a cikin sabuwar shekarar 2026. 

A cikin saƙonsa na sabuwar shekara, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa shekarar 2026 za ta kawo ci gaba mai yawa, zaman lafiya mai ɗorewa da kuma ci gaban jihar baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana cewa zaman lafiya yana dawowa sannu a hankali a Jihar Katsina bayan ƙoƙarin gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

“Wasu daga cikin ƙananan hukumominmu da ke kan gaba a hare-haren ‘yan bindiga, waɗanda ɓarayin daji suka yi wa ta’addanci a baya sun samu raguwar ayyukan ta’addanci. Muna da ƙwarin gwiwa cewa shekarar 2026 za ta kawo ƙarin ci gaba a fannin tsaro,” inji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaron ƙasa, Jami’an tsaron C-Watch, masarautun gargajiya da kuma mazauna jihar bisa haɗin kai da suka bayar wajen yaƙi da rashin tsaro. Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana ɗimbin kuɗaɗe da gwamnatinsa ta zuba a fannin ilimi, ciki har da samar da tallafin karatu, ginawa da gyaran ajijuwa da kuma rarraba kayan koyo da koyarwa na miliyoyin naira a makarantun jihar.

Ya kuma bayyana cewa, ‘Shirin Building Your Future’ ya ba da fifiko ga ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa, tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da aka hana shi samun ingantaccen ilimi saboda rashin kuɗi. 

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da ayyukan sabunta birane a gundumomi uku na majalisar dattawa, ciki har da gina hanyoyi da sauran gine-ginen more rayuwa.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa jihar gwamnati za ta ƙaddamar da ƙarin manyan ayyuka a shekarar 2026, wanda zai sauya yanayin biranen Katsina da ma karkara don su yi daidai da cigaban duniya don cimma ingantacciyar rayuwa. 

Raɗɗa ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba a fannin noma da kiwon dabbobi, tare da tallafa wa manoma don cimma nasarar girbe amfanin gona mai yawa. 

“Tallafin noma da muka bayar ya taimaka wajen magance matsalar ƙarancin abinci kuma ya ƙarfafa dubban mata. Za mu ci gaba da tallafawa manomanmu da masu kiwon dabbobi don tabbatar da cewa Katsina tana iya ciyar da kanta tare da ba da gudummawa don samar da abinci a ƙasar nan,” inji shi.

Gwamnan ya kuma bayyana gagarumin ci gaba a fannin kiwon lafiya, ciki har da samar da motocin ɗaukar marasa lafiya 15 da aka cika su da magunguna, tare da samar da babura masu ƙafa uku don su riƙa zagaya dukkan gundumomi 361.

Ya kuma bayyana cewa ana inganta cibiyoyin kiwon lafiya na farko inda suke aiki na tsawon awanni 24, tare da ɗaukar ma’aikata don ci gaba da tallafa wa ayyukan kiwon lafiya.

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana cewa ya zagaya dukkan ƙananan hukumomi 34 dake jihar don buɗe wasu ayyuka tare da sauraron koken al’umma. 

“Ra’ayoyin da mutanenmu suka bayar a lokacin rangadina da na gudanar za su tabbatar da ayyukanmu a shekarar 2026. Mun saurari al’umma, mun rubuta buƙatunsu kuma za mu aiwatar da su,” inji gwamnan.

By ukarofi