Kotu ta ƙi dakatar da ƙaramin Ministan Man Fetur daga raba rijiyoyin mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da aka shigar domin hana ƙaramin Ministan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur (ɓangaren Mai), Heineken Lokpobiri, da wasu hukumomi raba wasu rijiyoyin mai da filayensa, inda kotun ta umurci waɗanda ake ƙara da su fito su bayyana dalilin da ya sa ba za a amince da buƙatar ba.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke wannan hukunci yayin sauraron buƙatar gaggawa da kamfanonin mai na Hi-Reɓ da Hi-Reɓ Eɗploration and Production suka shigar, ta hannun lauyansu Ambrose Unaeze.

A maimakon bayar da umarnin dakatarwa, kotun ta umurci waɗanda ake ƙara da su fito su nuna hujjoji.

Mai shari’a Nwite, wanda ke zaman alƙalin hutu, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 5 ga Janairu domin sauraron bayanan waɗanda ake ƙara.

Waɗanda ake tuhuma a shari’ar sun haɗa da Ministan Man Fetur, Babban Lauyan Tarayya (AGF), da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NUPRC).

Kamfanonin da suka shigar da ƙara sun nemi kotu ta hana gwamnati sayarwa ko raba filayen mai da suka haɗa da Yorla South a Jihar Ribas, Akiapiri da Diebu Creek East a Jihar Bayelsa, da Idiok a Jihar Akwa Ibom, suna masu cewa filayen na maye gurbin wasu filaye da aka taɓa ba su amma daga baya aka kwace.

A cewar lauyansu, kamfanonin sun taɓa samun rabo a filin Utapate da OPL 2002, amma gwamnati ta janye su ba tare da dalili mai gamsarwa ba, duk da cewa an cimma yarjejeniyar sulhu wadda kotu ta amince da ita a matsayin hukunci.

A cikin takardar rantsuwa, daraktan kamfanonin, Chief Feliɗ Ezeamama, ya bayyana cewa sun ɗauki manyan matakai, sun biya wani ɓangare na kuɗaɗen lasisi, tare da gabatar da cikakken tsarin gine-ginen matatar mai mai iya tace ganga 50,000 a kullum a Akwa Ibom, wanda hukumomi suka amince da shi.

Ya ce, duk da alƙawuran da aka yi musu na maye gurbin filayen da aka janye, daga bisani an sake sayar da su ga wasu kamfanoni, lamarin da ya janyo musu asara mai yaea. A cewarsa, idan aka bar gwamnati ta ci gaba da raba waɗannan filayen, kamfanoninsu za su fuskanci babbar asara da tauye haƙƙoƙinsu na doka.

Kotun ta ce, dole ne ta ji ɓangaren gwamnati kafin zaukar mataki na gaba a shari’ar, domin tantance sahihancin hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar.

By ukarofi