Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban babban kwamitin shirya maulidin Sheikh Hadi Balarabe ya tabbatar da haka ga manema labarai a babban ofishin ƙungiyar Munazzamatul Fitiyanul Islam a Katsina.
Sheikh Hadi Balarabe ya bayyana cewa shine karo na uku da jihar Katsina ke karɓar wannan babban taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass.
Sheikh Hadi Balarabe ya cigaba da cewa a bana za a fara gudanar da taron masana da ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa, wanda za a kwashe tsawon kwanaki biyar ana yin sa, wanda masana daga ƙasashen duniya za su samu halarta domin gabatar da maƙaloli da suka shafi rayuwar shahararren malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Inyass.
Haka zalika za a gudanar da babban taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass a filin Wasa na tunawa da Sarkin Katsina, Marigayi Muhammadu Dikko dake cikin garin Katsina.
Shugaban kwamitin ya tabbatar wa mahalarta wannan gagarumin taron maulidin cewa kwamitin ya shirya tsaf domin samar da tsaron lafiya da dukiyoyi da samar da masauki ga manyan baƙi da duk wani abu da ake buƙata.
“Muna kira ga waɗannan ɗinbin baƙi da su zamanto masu bin doka da oda, domin a samu a gudanar da taron lafiya a kuma tashi Lafiya.
