Gobara ta lanƙwame gidan ruwa a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

Gobara ta afku a gidan ruwan tsohon ɗan majalisa, marigayi Ibrahim Mu’azzam da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano sakamakon tartsatsin wutar lantarki.

Ɗan marigayin, Nura Ibrahim Mu’azzam wanda ya bayyana haka, ya ce gobarar ta yi sanadiyar asarar abubuwa da dama a gidan ruwan.

Sanarwar dai ta Nura Ibrahim Mu’azzam, ta bayyana cewa wannan gobara ta jefa iyalai da maƙwabta da dama a cikin tsananin firgici.

Amma, duk da haka, mazauna yankin sun yi gaggawar kai dauki domin hana wutar yaduwa zuwa wasu gidaje.

Hukumar kashe gobara ta Bichi ta yi nasarar daƙile wutar kafin ta ƙara yaɗuwa zuwa wasu sassan gidajen da ke kusa.

“An yi dace babu mutane a cikin gidan, sun fita an kulle gidan kuma babu motoci a ciki. Da ta fara ci mutane suka gani sai suka yi yunkurin shiga gidan suka gan shi a kulle, sai suka haura suka samu balla get din ta ciki suka fara zuba wa wutar ruwa da yake akwai ruwan kwata a gidan sai suka rika diba suna watsawa kafin zuwan ‘yan kwana-kwana. To inda Allah dai ya kiyaye ba mutane, amma ta yi barna sosai gaskiya.” Nuna Ibrahim Mu’azzam Bichi.

Bisa haka, al’umar yankin sun yi kira ga jama’a da su rika yin taka-tsantsan, musamman wajen amfani da wutar lantarki da sauran abubuwan da ka iya haddasa gobara. Haka kuma, an yi kira ga shugabanni da kungiyoyi su tallafa wa Hukumar Kashe Gobara da kayayyakin aiki domin inganta aikinsu da kare dukiyoyin jama’a.

“Muna jan hankali ga Gwamnati akan ta samar mana da mota mai kysu ta kwana-kwana saboda wannan ta dade, tun lokacin zamanin Gwamna Shekarau aka ba da ita kuma ta tsufa, ba ta aiki yadda yakamata. Don haka muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana da wannan mota”, inji Nura Ibrahim Mu’azzam Bichi.

By Babaji