Kwankwaso ya musanta goyon bayan zargin komawar Abba APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jagoran Jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya amince tare da bada goyon baya ga shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyya mai mulki, APC.

Hakan na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa Abba na shirin fita daga NNPP domin koma wa APC, lamarin da ya sa aka shiga fargaba acikin jam’iyyar da tunanin Kwankwaso ka iya sassauto adawarsa ta yawan sauye-sauyen sheƙar ‘yan siyasa a Nijeriya.

A daren Talata wayewar Laraba ne aka samu wasu rahotanni a kafafen sada zumunta da ke ikirarin Kwankwaso ya sauya matsaya kuma ya amince wa gwamnan da sauran ‘yan NNPP su koma APC.

To amma wannan batu bai samu karɓuwa ba domin ‘yan ɓangaren tsohon gwamnan ta bakin mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, sun ce jagoran bai goyi baya ko amincewa da wannan yunƙuri ba, saboda har yanzu shi da gwamnan suna biyayya ga tsare-tsaren NNPP da ra’ayoyin jama’a.

A cewar sanarwar, an zaɓi Abba ne a ƙarƙashin tutar NNPP kuma har yanzu yana riƙe da amanar jam’iyyar da ta al’ummar da suka zaɓe shi.

Ta bayyana ikirarin da aka jingina wa jagoran a matsayin yunƙurin ruɗar da jama’a ta amfani da labaran ƙarya, inda ta yi kira da a ƙaurace wa zancen.

Haka ma Sakataren Jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya ce an ƙirƙiri zancen ne da nufin yaɗa tunanin cewa Kwankwaso ya sanya albarka ga yunƙurin da jam’iyyar ba za ta taɓa amince da shi ba, wanda ka iya zama nau’i na zagon-ƙasa ga harkokinta.

By Babaji