Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya samu gurbin karatu a Jami’ar Northwest University, Kano, kamar yadda jami’ar ta sanar a ranar Litinin.
A wata takarda da Jafaru Sule Muhammad, shugaban sashen jarrabawa, karɓar ɗalibai da adana bayanai ya sanya wa hannu a madadin magatakarda, an bayyana cewa sarkin ya samu gurbin karatu a fannin Shari’a (LL.B. Common Law and Sharia) a matakin Level 200, daga zangon karatu na 2024/2025.
Takardar, wacce aka aika zuwa Gidan Rumfa Kano, ta ce an amince da shigar sarkin ne bayan ya cika sharuɗɗan jami’a na karɓa ta musamman, tare da neman ya bi ƙa’idoji da dokokin jami’ar wajen yin rajista.
Sanusi II, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kammala digirinsa na farko a fannin tsumi da tanadi (Economics) a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1981, ya yi NYSC a Yola, sannan ya samu digirin na biyu masters a shekarar 1983.
Daga bisani kuma ya yi karatun ilimin addinin Musulunci a Khartoum.
A shekarar 2024, Sarkin ya samu digirin PhD a Shari’ar Musulunci daga Jami’ar SOAS, University da ke Landan, inda ya mayar da hankali kan dokokin iyali na Musulunci da gyaran al’umma.
