NYSC ta sauya ‘yan hidimar ƙasa 2,050 zuwa Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta tura ɗalibai guda 2,050 zuwa Jihar Bauchi na rukunin ‘A’ kuma zango na 1 a 2026.

Kodinetanta na jihar, Kufre Umoren a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya bayyana haka a yau Talata.

A cewarsa, za a fara rajista daga ranar 21 ga Junairu kuma a kammala a 23 ga watan Junairu a sansanin NYSC da ke yankin Wailo a Ƙaramar Hukumar Ganjuwa ta jihar.

Ya bayyana cewa, za a fara aikin wayar da kan ‘yan hidimar ne a ranar 23 ga Junairu, yayin da za a kammala a ranar 10 ga watan Fabarairu.

Umoren ya kuma ce, za a bai wa kowane ɗalibi damar shiga sansanin ne bayan an tantance shi a matsayin halastaccen wanda ya kammala kararun da ake buƙata ga sabon shiga a hidimar ƙasa.

Ya ƙara da cewa, za a yi tantancewa mai faɗi tare da horar da ‘yan hidimar ga ƙaurace wa ayyukan sojan gona da ababen ka iya haifar musu da tsaiko yayin hidimar.

Kazalika, ya kiraye su da su kiyaye ƙa’idoji da dukkan sharuɗɗan da aka gindaya, yana mai cewa za a hukunta dukkan wanda aka samu da saɓa wa dokokin hukumar.

By Babaji