‘Yan sanda sun ƙaryata rahoton garkuwa da masu bauta sama da 100 a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Rabi’u, ya bayyana rahoton sace masu bauta sama da guda 100 a Ƙaramar Hukumar Kajuru a matsayin ƙarya da dillalan rikicin suka tsirar da nufin haddasa fitina a jihar.

Wasu rahotanni a jiya Litinin sun yi ikirarin ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da sama da mutane 100 a lokacin da suke tsaka da addu’o’i a coci a Ƙauyen Kurmin Wali da ke Kajuru, ranar Lahadi.

Da yake ganawa da manema labarai a yayin zaman majalisar tsaro ta jihar a ɗakin taro na Sir Kashim Ibrahim, ranar Litinin, Kwamishinan ya ƙalubalanci da a bada sunayen waɗanda aka ce an sacen da wasu ƙarin bayanai akansu domin a tabbatar da gaskiyar labarin.

Ya gargaɗi masu yaɗa ire-iren jita-jitar da su ƙaurace wa dukkan abin da ka iya zama takala ga zaman lafiyar al’ummar jihar, yana mai cewa doka za ta yi aiki akan dukkan wanda aka samu da aikata irin laifin.

A nasa jawabin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Dauda Madaki ya ce a lokacin da suka ji jita-jitar, sai ya tara jami’an ƴan sanda da na wasu hukumomi, waɗanda zuwansu Kurmin Wali ke da wuya, sai suka gano babu wani hari da aka kai a yankin.

“Mun ziyarci cocin da aka ce a nan aka yi garkuwar. Babu wata shaida ta wani hari. Na tambayi Mai garin ƙauyen, Mai Ɗan Zaria, sannan ya tabbatar da cewa babu wani hari irin haka da ya faru”, inji Madaki.

Baya ga haka, ya kuma yi bincike daga ɓangaren wasu mutane, amma babu wanda ya ce an samu aukuwar harin da sahihan bayanai, yana mai shawartar al’ummar yankin da su cigaba da zama cikin kwanciyar hankali da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin walwala.

Kazalika, ya kiraye su da ruwaito wa hukuma dukkan wani abin zargi a yankunansu domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya ga rayuka da dukiyoyinsu.

By Babaji