Kaduna: ’Yan bindiga sun nemi miliyan N28.9 kafin fara tattaunawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu ’yan bindiga da suka sace ɗaruruwan ’yan coci a ƙaramar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna sun buƙaci a biya su kuɗin babura da suka ce sun ɓata kafin su fara tattaunawar sakin mutanen da suke hannunsu.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yi iƙirarin cewa babura 17 nasu ne suka ɓace a lokacin wani farmaki da jami’an tsaro suka kai a yankin, inda suka ce kowanne babur na da darajar Naira miliyan N1.7, wanda ya haɗa jimillar kuɗin da suka nema zuwa Naira miliyan N28.9.

Sun ce dole ne a biya wannan kuɗi gaba ɗaya kafin su bayyana adadin kuɗin fansa da za su nema domin sakin waɗanda suka sace.

Lamarin ya faru ne bayan wani hari da aka kai kan coci-coci uku a safiyar Lahadi a yankin Kurmin Wali, inda aka sace mabiya coci 177 a yayin ibada.

Daga baya mutum 11 sun samu tserewa, lamarin da ya bar mutum 166, ciki har da mata da ƙananan yara, a hannun masu garkuwa.

Shugabannin al’umma da iyalan waɗanda aka sace sun bayyana cewa buƙatar biyan kuɗin baburan ta jefa su cikin sabon tashin hankali, ganin cewa wannan kuɗi ba ya cikin kuɗin fansar da za a iya nema daga baya.

Wani mazaunin yankin, Linus Abu, ya ce saɓanin wani hari da aka kai a ranar 11 ga Janairu inda aka nemi kuɗin fansa kai tsaye, wannan karon ’yan bindigar sun fara da buƙƙtar diyya kan baburan da suka ce sun ɓata.

Sarkin ƙauyen Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun tuntuɓi wani mai shiga tsakani inda suka nace cewa dole ne a dawo da baburan ko a biya kuɗinsu kafin a saki mutanen.

Ya ce sun kuma zargi wasu mazauna yankin da cire wasu sassan baburan, lamarin da ya ƙara tsananta tattaunawar.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro sun fuskanci suka daga mazauna yankin da shugabannin addini, musamman bayan da aka fara musanta rahoton sace-sacen kafin daga baya shugaban ƙungiyar CAN na arewa ya tabbatar da faruwar lamarin. 

Gwamnan jihar, Uba Sani, ya kai ziyara Kurmin Wali ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, inda ya jajanta wa al’umma tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da jami’an tsaro domin ganin an sako waɗanda aka sace cikin gaggawa.

Lamarin na ƙara jaddada tsananin matsalar tsaro a yankin, tare da tayar da tambayoyi kan yadda za a kawo ƙarshen sace-sace da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a arewacin Nijeriya.

By ukarofi